Ministan Ma’adinai da Ƙarafa, Shuaibu Audu, ya yi alƙawarin farfaɗo da Masana’antar Ƙarafa ta Ajaokuta.
Audu ya yi wannan alƙawarin a ranar farko da ya fara shiga ofis, a matsayin sabon Ministan Harkokin Ƙarafa.
Ya ce akwai matuƙar buƙatar a farfaɗo da Ajaokuta Steel, domin Najeriya ta riƙa samar da ƙarafa.
Ya ce zai tsara manhajar bunƙasa harkokin ƙarafa, domin ya tabbatar da fara aikin farfaɗo da Masana’antar Ƙarafa ta Ajaokuta, ba tare da wani ɓata lokaci ba.
An gina Masana’antar Ƙarafa ta Ajaokuta a cikin Jihar Kogi, tsakanin 1979 zuwa 1990s, sai dai kuma tuni wurin ya tashi daga masana’antar ƙarafa ya koma ƙarambosuwa.
Cikin Satumba na shekarar 2022, gwamnatin tarayya ta amince za ta biya wani kamfanin Indiya Dala Miliyan 496, domin raba shi da haƙƙin mallakar masana’antar, don ta koma mallakin Gwamnatin Tarayya.
Gwamnatin marigayi Umaru ‘Yar’Adua ce ta soke cinikin cefanar da Ajaokuta Steel da Kamfanin Haƙar Ma’adinai na Iron One Mining Company da ke Ore.
Da ya ke magana a ranar Litinin, sabon Ministan Ƙarafa Audu ya ce burin wannan gwamnatin ne a farfaɗo da masana’antun yadda za a riƙa sarrafa ƙarara a cikin gida Najeriya.
Sai dai kuma wani babban ƙalubalen da ministan zai fuskanta, shi ne yawan masu haƙo ma’adinai birjik a cikin dazukan ƙasar nan ba bisa ƙa’ida ba.
Sau da dama ana danganta matsalar tsaron wasu yankuna da haƙar ma’adinai da ake yi a can.
Discussion about this post