Sabon Ministan Tsaro, Abubakar Badaru da Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, sun kama aiki a ranar Talata.
Kowanen su iya shiga ofis a Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa, Abuja, inda Badaru ya karɓi mulki daga hannun Ibrahim Kana, Babban Sakatare na Ma’aikatar Tsaro ta Ƙasa.
A jawabin sa na farkon kama aiki, Badaru ya ce zai bi diddigin rahotannin matsalar tsaro da aka riƙa bayarwa a baya.
Ya ce ta hakan zai shawo kan matsalar tsaron da ta yi wa ƙasar nan harshen-damo.
Ya ce ba za su taɓa cin amanar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ba su ba. Saboda haka ya umarci Manyan Hafsoshin Tsaron Ƙasa su ba shi jadawalin lokacin da su ke gani za a daƙile matsalar tsaro a faɗin ƙasar nan.
“Idan sun ba ni lokacin da za a kawo ƙarshen matsalar tsaro, ni ma zan kai wa Shugaban Ƙasa, kuma na tabbatar zai riƙa sa-ido a kan mu.
“A shirye Shugaban Ƙasa ya ke domin ya ba mu duk wani goyon bayan da ya wajaba, domin mu yi nasara. Saboda shi nasara kawai ya sani, bai san wani abu rashin nasara ba.
“Saboda mun san idan babu tsaro a ƙasar nan, to babu masu zuba jarin da za a samu kafa masana’antu. Idan babu masana’antu kuwa, to babu ci gaban tattalin arziki kenan.” Inji Badaru.
Badaru ya sha alwashin cewa za a samu gagarimin ci gaba a fannin tsaro a lokacin sa. A kan haka ne ya ce mutane su daina zolaya da yi wa naɗin su habaici.
Discussion about this post