Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC), ta bayyana an yi asarar rayuka har 4,387 daga watan Janairu zuwa Yuni, 2023.
Adadin ya ƙunshi na yawan haɗurran da aka yi a jihohi 36 da Gundumar FCT Abuja a cikin watannin shida.
Babban Jami’in Hukumar FRSC mai suna Bisi Kazeem ne ya bayyana hakan, a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai, ranar Lahadi a Abuja.
“Tsakanin Janairu zuwa Yunin wannan shekarar, an yi asarar rayuka 4,387 a haɗarin motoci daban-daban a Najeriya.
“FRSC ta kuma tantance mutum 14,108 ne su ka samu raunuka a haɗurra daban-daban cikin watannin shida.
“Yawancin haɗurran na faruwa ne sanadiyyar tafiye-tafiyen dare, gajiya, karya dokokin tuƙi, wuce mota a wurin da bai dace ba, tuƙin ganganci, tayoyin da ba masu inganci ba ko waɗanda su ka ɗashe, da kuma gudun-wuce-sa’a.
“To kuma ka san jami’an FRSC ba su aiki cikin dare. Wannan ya sa direbobi na amfani da wannan damar su na karya dokokin tuƙi sosai a cikin dare.” Inji shi.
Kazeem ya ce hukumar su ta ceto rayukan fasinjoji 15,789 ba tare da sun ji ciwo ba a cikin watanni shida.
Sai dai kuma ya ce an samu raguwar yawan haɗurran manyan tireloli da tankoki.
Ya ce tsakanin Janairu zuwa Yuni, samu yawan haɗurra har 4,691.
Discussion about this post