Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump, ya kai kan sa kurkuku, inda ya isa garin a cikin jirgin sa ƙirar Boeing 757.
Magoya bayan sa na kiran jirgin da suna Trump Force One. Bayan saukar jirgin a filin jirgin Georgia, ya sauko ƙasa, ya sauko ƙasa, inda ya samu rakiyar jerin gwanon helikwaftoci waɗanda su ka yi tafiya a sama tsawon kilomita 22 zuwa Kurkukun Fulton.
Ya isa kurkukun ƙarfe 7:30 na dare agogon EST. An yi masa rajistar dangwala yatsa, daga nan aka tsare shi.
Kafin ya yi saranda, an bayar da belin Trump ga lauyoyin sa kan kuɗi Dalar Amurka 200,000.
Trump ya biya kashi 10% bisa 100% na kuɗin belin ga wani kamfanin ajiyar kuɗaɗen beli.
Ya shafe mintina 20 a kurkukun, daga nan kuma ya hau helikwafta zuwa birnin Atlanta, inda ya hau jirgin sa ya sake komawa gidan sa da ke birnin New Jersey.
Kafin zuwan Trump kurkuku, wasu sanatocin Republican sun yi maƙabalar neman takarar shugaban ƙasa.
Sai dai ba su sha da daɗi ba, saboda ‘yan kallo sun riƙa yi masu sowa, tare da surfa masu baƙaƙen kalamai.
Hakan kenan ya na nufin har yanzu Trump na da sauran karsashin iya sake fitowa takarar zaɓen shugaban ƙasa na 2024.
Discussion about this post