Sojojin da suka ƙwace mulki a Jamhuriyar Nijar sun bayyana kafa sabuwar gwamnati, sa’o’i kaɗan kafin fara taron Shugabannin ECOWAS da aka shirya yi yau Alhamis, a Abuja.
A Yamai, an bayyana kafa sabuwar gwamnati da rana, mai ɗauke da Ministoci 21.
Wannan sanarwa ta zama tamkar yin kunnen-uwar-shegu ga gargaɗin da ECOWAS ta yi wa ƙasar ita da wasu ƙungiyoyin ƙasashen duniya, cewa su gaggauta mayar da Mohammed Bazoum a kan kujerar mulkin sa.
A yau Alhamis ECOWAS ke sake zaman duba mataki na gaba da za su sake ɗauka a kan Nijar.
Lamarin ya zo daidai da lokacin da a cikin gida Najeriya ake ci gaba da kiraye-kirayen ba a yarda Najeriya ko ECOWAS su kai wa Nijar hari ba.
Sabuwar Gwamnatin Nijar: Gamin Gambizar Sojoji Da Farar Hula:
Sabuwar Gwamnatin Nijar dai ta ƙunshi sojoji da fararen hula, a ƙarƙashin Firayi Minista Lamine Zeine Ali Mahamane, wanda kuma shi zai zama Minsiatan Tattalin Arzikin Ƙasa da Harkokin Kuɗaɗe.
Tsohon Shugaban Ma’aikata Salifou Mody, wanda Laftanar Janar ne Mai Ritaya, wanda ake sa rai zai zama Mataimakin Shugaban Juyin Mulki, Janar Tchiani, shi ne aka naɗa Ministan Tsaron
Ƙasa.
Abdourahmane Amadou, wanda ya yi suna wajen karanta jawaban mahukunta sojan Nijar a gidan talabijin, shi aka naɗa Ministan Matasa da Wasanni.
Tuni dai dama suka naɗa sabbin hafsoshin tsaron ƙasa, kuma suka kori manyan jami’an gwamnati waɗanda suka yi aiki a ƙarƙashin gwamnatin Bazoum.
Discussion about this post