A Ranar Juma’a ce Sojojin Mulkin Nijar a ƙarƙashin jagorancin Janar Abdourahmane Tciani ta bai wa Jakadan Faransa na Nijar wa’adin ficewa ya bar ƙasar.
Cikin wata wasiƙa daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijar, wadda aka aika wa Ma’aikatar Wajen Faransa, an buƙaci Jakada Sylvain Itte ya fice daga Nijar cikin sa’o’i 48, wato kwanaki biyu kenan.
Mahukuntan Nijar sun bada dalilin korar Jakadan Faransa dacewa ya ƙi zuwa ya amsa gayyatar tattaunawa da shi da mahukuntan na Nijar su ka ce za su yi.
“Akwai dalili kuma na wasu abubuwa da Gwamnatin Faransa ke yi, waɗanda ba alheri ba ne ga al’ummar Nijar.”
Wannan bayani duk ya na ƙunshe cikin dalilan da Nijar ta ce su ka haddasa ta kori Jakadan Faransa.
Tsananin shauƙin tsanar ƙasar Faransa dai sai ƙara ruruwa yake yi a cikin zukatan ‘yan Nijar, tun bayan kifar da Gwamnatin Farar Hula ta Mohammed Bazoum.
Tun ba a daɗe da yin juyin mulkin ba sai da gungun hasalallun masu tsabar ƙasar Faransa su ka kai wa Ofishin Jakadancin Faransa da ke birnin Yamai hari.
Hasalallun waɗanda ke goyon bayan Sojojin Mulki, sun riƙa filfila tutar Rasha a lokacin da su ke zanga-zangar.
Korar Jakadan Faransa daga Nijar alama ce da ke nuna munin zaman doya da manjan da ake yi tsakanin Nijar da tsohuwar uwargijiyar ta, Faransa.
Korar Jakadan Faransa Daga Nijar:
Sai dai kuma Ofishin Ma’aikatar Harkokin Wajen Faransa ya ce ai Jakadan Faransa da ke Nijar an tura shi ne tun ƙarƙashin halastacciyar gwamnatin Bazoum. Don haka sojojin mulkin Nijar kuma haramtacciyar gwamnati ce.
Sai dai ta ce a koda yaushe ta na duba yanayin tsaro a Nijar a batun da ya shafi ofishin jakadancin Faransa ɗin da ke Nijar.
Discussion about this post