An aza ranar da dakarun ECOWAS za su kutsa cikin Nijar, su afka wa ƙasar da yaƙi, domin a ƙwato mulki hannun sojoji, a maida wa farar hula. Haka dai Manyan Hafsoshin Tsaron ECOWAS ɗin su ka bayyana a ranar Juma’a.
“Mun aza rana. Kuma mun amince dangane da abin da za a buƙata wajen kai harin,” haka Aljazeera ta ruwaito Kwamishinan Harkokin Siyasa, Zaman Lafiya da Tsaro na ECOWAS, Abdel-Fatau Musah ya bayyana.
Duk da dai bai bayyana kowace rana ba ce, ko sauran kwana nawa nan gaba, ya ƙara da cewa “mun shirya afka wa Nijar a duk lokacin da aka bayar da oda.”
Manyan Hafsoshin Tsaron ECOWAS sun yi taron kwana biyu a Accra, babban birnin ƙasar Ghana, domin tattauna yadda za haɗa rundunar afka wa Nijar.
ECOWAS ta yi gargaɗin afka wa Nijar idan duk wata hanya ta diflomasiyya da lalama ta faskara.
A ranar Juma’a, Musah ya ce ECOWAS har yanzu a shirye take a shiga tsakani ta hanyar samun sasanci. “Don haka ba mu kulle ƙofar sasantawa ba.”
“Kowa ya ma daina tantama cewa idan duk wasu hanyoyin sasanci su ka faskara, to fa zaratan yaƙin Afrika ta Yamma a shirye su ke da su amsa kiran aikin afka wa Nijar.” Haka Aljazeera ta ce Musah ya faɗi.
Kai Wa Nijar Hari: Ƙasashen Cape Verde, Mali, Burkina Faso, Guinea Ba Su Goyon Bayan Afka Wa Nijar Da Yaƙi:
Ƙasashen Cape Verde, Mali, Birkina Faso da Gini sun nuna rashin amincewa a afka wa Nijar da yaƙi.
A Najeriya dai Majalisar Dattawa da ɗaukacin al’ummar ƙasar ba su goyon baya.
Haka su ma manyan malaman Najeriya sun nuna rashin goyon bayan su, kuma sun yi ƙoƙarin su wajen shiga tsakani, domin a sasanta ba tare da zubar da jini ba.
Discussion about this post