An bayyana cewa ECOWAS ba ta fidda ran afka wa Jamhuriyar Nijar da yaƙi ba, domin kawar da sojojin juyin mulki, a dawo da dimokraɗiyya a ƙasar.
Yayin da ake ƙoƙarin sasantawa, a gefen Nijar dai har yau ta hau kan kujerar-na-ƙi, bayan cikar wa’adin ECOWAS.
A na ta ɓangaren kuma, Najeriya ta ƙara tsaurara matakan takunkumi kan Nijar, inda aka Babban Bankin Najeriya (CBN), umarnin riƙe kuɗaɗen duk wani mai dangantaka da mahukuntan sojan Nijar ko mai goyon bayan su.
Kakakin Yaɗa Labaran Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, Ajuri Nyerale ne ya bayyana haka a ranar Talata yamma, tare da cewa akwai ma wasu tsauraran takunkumin na zuwa kan Nijar daga ɓangaren ECOWAS.
Ngelare ya shaida wa ‘yan jarida cewa “ECOWAS ba ta yanke shawarar ƙin afka wa Nijar da hare-haren ƙwace mulki daga hannun sojoji ba. Kuma za ta tattauna hakan a taron musamman na gaggawa da ta yi a Abuja, ranar Alhamis.”
A wani labarin kuma, Nijar ta hana UN, AU da ECOWAS shiga ƙasar, ta hana Amurka ganin Shugaban Mulkin Soja.
Mahukuntan mulkin sojan Jamhuriyar Nijar sun watsa wa Majalisar Ɗinkin Duniya da Ƙungiyar Tarayyar Turai da ECOWAS ƙasa ido, yayin da su ka hana watagar haɗin guiwar su shiga ƙasar su tattauna hanyoyin sulhuntawa.
Wata wasiƙar da Ma’aikatar Tsaron Nijar ta rubuta, ta ce manyan ƙungiyoyin uku sun nemi tawagar su ta je ranar Talatar jiya kenan.
A kan haka ne Nijar ta sanar da su cewa tunda dai ECOWAS ta umarci ƙasashen ta da su ka haɗa iyaka da Nijar su rufe iyakokin su, saboda haka ƙyale wannan tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya da EU su keta sararin samaniyar Nijar, abu ne na musamman mai buƙatar nazarin musamman daga mahukuntan Nijar.
Wasiƙar wadda ta faɗo hannun PREMIUM TIMES, ta na kuma ɗauke da cewa sai mahukuntan Nijar sun bada iznin cewa dokar hana keta sararin samaniya bai shafi wannan tawagar ba, to kuma babu hakan a cikin doka.
A cikin wasiƙar da UN ta aika wa Nijar, an shirya cewa tawagar wakilan ƙungiyoyin uku za su isa Nijar ranar 8 Ga Agusta, a cikin jirgin musamman wanda UN ta yi shata.
“Kuma sun ƙara jaddada shirin su na tattaunawa da mahukuntan Nijar, wanda tawagar UN ɗin ta ce za ta ɗora kamar yadda jagoran ta ECOWAS, Abdulsalami Abubakar ya fara nunawa, sai dai ita kuma Nijar ba ta maraba lale da zuwan tawagar a wannan lokacin, saboda dalilin tsaro.”
A kan haka ne Nijar ta ce tilas sai dai a ɗaga batun shirya tsron, wanda ta ce ganawa da wasu wakilan cikin tawagar ba abu ne mai yiwuwa ba a yanzu, daidai lokacin da ake kumfar-bakin kai wa Nijar farmakin soja.
Daga nan Nijar ta buƙaci Wakilin ECOWAS a Yamai ya sanar da ECOWAS cewa matsala ba daga Nijar ɗin ba ce, domin ita mai nuna haɗin kai ce.
Idan ba a manta ba, mahukuntan Nijar sun hana tawagar ECOWAS ƙarƙashin Abdulsalami Abubakar da Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ganawa da Shugaban Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani, ko hamɓararren Shugaban Ƙasa, Mohammed Bazoum.
Ɗan Hakin Da Ka Raina Shi Ke Tsone Maka Ido: Nijar Ta Hana Amurka Ganin Shugaban Juyin Mulkin Ƙasar:
Ana wata kuma sai ga wata, Mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Victoria Nuland, ta kai ziyara Yamai a ranar Litinin, amma ita ma ba a bari ta yi ido-da-ido da Shugaban Mulkin Sojan Kasar ba.
Yayin da ake wannan dambarwa, mahukuntan Nijar na ci gaba da samun goyon bayan al’ummar ƙasar, waɗanda ke yin tir da ƙasashen da ke zuguguta a kai masu harin soja.
Har yanzu dai ba a san halin da hamɓararren Shugaban Ƙasa Bazoum ke ciki ba, tun bayan wani bayani da ya yi a cikin shafin sa na Tiwita a makon da ya gabata.
Ita kuwa ECOWAS ta shirya yin zama na musamman a Abuja ranar Alhamis mai zuwa, yayin da wa’adin neman saukar sojojin Nijar daga mulki ya cika tun a ranar Lahadi.
A cikin Najeriya ma dai ‘yan ƙasar musamman Arewacin ta da kuma Majalisar Dattawa sun nuna rashin amincewa a yi amfani da ƙarfin soja kan Nijar.
Discussion about this post