Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Afrika (AU), ta bada sanarwar dakatar da Jamhuriyar Nijar daga cikin ƙungiyar. Majalisar Tsaron AU ce ta fitar da sanarwar dakatarwar, biyo bayan rigimar siyasar da ake ciki a ƙasar, bayan sojoji sun ƙwace mulki daga hannun hamɓararren Shugaban Nijar, Mohammed Bazoum.
“AU ta yanke shawarar dakatar da Jamhuriyar Nijar daga shiga duk wasu hulɗoɗi na ƙungiyar a Afrika baki ɗaya, har sai idan ƙasar ta koma kan mulkin Dimokraɗiyya tukunna.” Haka sanarwar da Bayyana.
Ba wannan ne karo na farko da AU ta fara dakatar da wata ƙasa ba, saboda dalilai na yin juyin mulki.
Ta dakatar da Mali, Gini, Burkina Faso, lokacin da sojoji suka kwace mulki ƙasashen uku.
Sai dai kuma wannan dakatarwar ba ta sa jin tsoron sake aiwatar da juyin mulki a wasu ƙasashen ba.
AU ta goyi bayan wa’adin makonni biyu da ECOWAS ta bai wa shugabannin sojojin mulkin Nijar cewa su sauka su maida Mohammed Bazoum kan kujerar sa.
Amma dai AU na duba sakamakon tura sojojin ECOWAS cikin Nijar zai haifar a ɓangaren tattalin arziki, zamantakewar rayuwa da kuma tsaro, tare da bada umarnin a kammala nazarin batun a maida wa AU ɗin domin ta duba.
A ranar Talata ce dai AU ta dakatar da Nijar, tare da yin kira ga ƙasashe, cibiyoyi da ƙungiyoyi na duniya su ƙaurace wa hulɗa da Nijar kuma su daina amincewa da shugabancin sojojin da su ka ƙwace mulki a hannun Bazoum.
AU ta la’anci juyin mulkin, sannan kuma ta nemi a saki Bazoum, sauran iyalan sa da kuma dukkan jiga-jigan gwamnatin sa waɗanda ake tsare da su.
“AU na aiki kafaɗa da kafaɗa da ECOWAS, domin tattara sunayen sojojin mulkin Nijar, fararen hular da ke goyon bayan su domin su ma a ƙaƙaba masu takunkumi. Duk mai hannu wajen tsare Bazoum shi ma takunkumin zai hau kan sa.”
Sannan kuma AU ta ce ba ta yarda kowace ƙasa daga wajen Afrika ta shigo yin tatsalandan da sojojin ta a rikicin Nijar ba.
Discussion about this post