Gwamnatin Tarayya ta janye ƙarar da ta kama Shugabannin Ƙungiyar Ƙwadago a makon da ya gabata.
A ranar Litinin ce gwamnati ta sanar da janye ƙarar, wadda ta shigar, har ta nemi a kulle shugabannin a kurkuku, saboda sun keta umarnin kotu, sun gudanar da zanga-zangar da kotu ta ce kada su yi.
Jedy-Agba ta bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ne ya shiga tsakani a cikin wata wasiƙar da ya aika wa lauyan NLC, Femi Falana.
Haka kuma wata sanarwa ta ce za a sake zama tsakanin NLC da kuma wakilan Shugaba Tinubu a ranar Alhamis.
Cikin makon jiya ne dai wannan jarida ta kawo rahoton cewa Gwamnatin Tarayya ta maka shugabannin NLC kotu, saboda bijire wa umarnin kotu.
Gwamnatin Tarayya ta fara tsara canje-canjen maka shugabannin Ƙungiyar ta Ƙasa, NLC da TUC kotu, saboda sun bijire wa umarnin kotu, sun fita zanga-zanga a ranar Laraba.
Tuni dai aka maka su a Kotun Shari’ar Ma’aikata ta Ƙasa, da ke Abuja a ranar Larabar da su ka shiga zanga-zangar.
Gwamnatin Tarayya ta nemi kotu ta ɗaure shugabannin NLC da TUC, saboda bijire wa umarnin kotu da su ka yi, wadda ta hana su shiga zanga-zanga, tun a makon jiya, amma su ka yi biris da umarnin.
NLC da TUC sun tsunduma yajin aiki da zanga-zangar a ranar Laraba, domin su nuna wa gwamnatin tarayya irin mawuyacin halin ƙuncin da masu ƙaramin ƙarfi ke fama, tun bayan cire tallafin fetur da aka yi.
An gudanar da zanga-zangar a Abuja, Legas da sauran manyan biranen jihohin ƙasar nan.
Tun a ranar 26 Ga Yuli dai Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi NLC da TUC cewa bijire wa umarnin kotu fa babban laifi ne, wanda hukuncin da shi ne ɗaure mutum a kurkuku.
Ganin yadda ƙungiyoyin ƙwadago su ka tashi da zanga-zanga a ranar Laraba, sai Ma’aikatar Harkokin Shari’a ta gaggauta zuwa kotu domin riƙon ta caji masu shirya zanga-zangar da laifin karya umarnin kotu.
An aika da wannan sammacin shigar da ƙara ga Shugaban NLC, Joe Ajaero, Mataimakan sa Audu Aruba, Adeyanju Adewale da Kabiru Sani.
Sai kuma Babban Sakatare, Emmanuel Ugboaja, sai Shugaban TUC Festus Osifo da Sakatare Nuhu Toro.
A na ta ɓangaren Majalisar Dattawa ta yi wa NLC da TUC alƙawarin magance buƙatun NLC cikin kwana bakwai.
Ganin yadda Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, NLC ta mamaye Majalisar Ƙasa a ranar Laraba, Majalisar Dattawa ta yi masu alƙawarin biya masu buƙatun su a cikin kwanaki bakwai masu zuwa.
Ƙungiyar ta Ma’aikatan Ƙwadago ta Najeriya ta mamaye harabar Majalisa a ranar Laraba, domin nuna fushi da damuwar su kan ƙarin tsadar rayuwa da aka afka a faɗin ƙasar nan, tun bayan hawa mulkin Shugaba Bola Tinubu.
Tinubu ya ƙara zafafa halin ƙunci da tsananin raɗaɗin tsadar rayuwa, tun a ranar da aka rantsar da shi, inda ya yi wa ‘yan Najeriya mummunan albishir na janye tallafin fetur nan take.
Masu zanga-zanga a Abuja sun darkaki Majalisar Dattawa a bisa jagorancin Shugaban NLC na Ƙasa, Joe Ajaero da Festus Osifo, Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa, TUC.
A cikin fushi su ka darkaki Majalisar Ƙasa daga wurin da suka fara yin mahaɗa da cincirindo, kusa da otal ɗin Trsnscorp.
Mamayar da su ka yi wa Majalisa ta tilasta an tsayar da tantance mai ministocin da Bola Tinubu ya aika da sunayen su, da ake ci gaba da tantancewa tun daga ranar Litinin.
Masu zanga-zanga sun ce ba su iya ciyar ciyar da iyalan su, har kuma a lokaci guda su iya fita zuwa wuraren aikin su.
Sun jaddada cewa malejin tsadar rayuwa ya cilla sama sosai, har lamarin ya yi matuƙar muni.
Sanatan Barno ta Tsakiya, Ali Ndume ne aka tura masu ya je ya ba su haƙuri, kuma ya roƙi masu zanga-zangar su bai wa Majalisar Dattawa kwanaki bakwai domin a biya dukkan buƙatu da ƙorafe-ƙorafen da su ka gabatar.
Ita ma Sanatar FCT Abuja, Ireti Kingibe, ta roƙi masu zanga-zangar su bada kwanaki bakwai domin su tabbatar an magance matsalolin da su ka haddasa zanga-zangar.
Ta ce a “wannan karon Majalisar Dattawa ba za ta watsa masu ƙasa a ido ba.”
Discussion about this post