Babban Kwamandan Dakarun Najeriya, Janar Taoreed Lagbaja, ya bayyana cewa Sojojin Najeriya za su fara lugude da rugugin kai hare-hare domin kakkaɓe ‘yan bindiga da dazukan yankin Zamfara.
Lagbaja ya bayyana hakan a lokacin da ya kai wa Gwamna Dauda Lawal ziyara a Gidan Gwamnatin Gusau, a ranar Litinin.
Janar Lagbaja ya je Zamfara a wani rangadi da ya ke yi cikin jihohin Arewa maso Yamma.
Kakakin Yaɗa Labaran Gwamnan Zamfara, Sulaiman Idris ne ya bayyana haka, cikin wata sanarwar da ya fitar.
“A yayin ganawar sa da Babban Kwamandan Dakarun Najeriya, Gwamna Dauda Lawal ya roƙi a ƙara tura sojoji a cikin Jihar Zamfara, domin su daƙile matsalar tsaron da ta ƙi ci, ta ƙi cinyewa a jihar.
“Lagbaja ya yi doguwar ganawa da Gwamna, inda su ka tattauna hanyoyin da za a ƙara ƙarfafawa, wajen haɗa hannu a kakkaɓe ‘yan bindiga a jihar.” Haka Idris ya jaddada, cikin wata sanarwar da ya aika wa PREMIUM TIMES.
Ya ƙara da cewa ziyarar wadda Babban Kwamandan Dakarun Najeriya ya kai Zamfara, ta ƙara nuna irin tashi tsaye da gwamnan ya yi wajen ganin an magance matsalar tsaron da ta ƙi ci, ta ƙi cinyewa a jihar.
“Haka kuma za ta ƙara ƙarfafa guyawun sojojin da ke ci gaba da fafata kai wa mahara farmaki a cikin dazukan Zamfara.
“Lagbaja ya tabbatar wa Gwamna Lawal cewa nan da ‘yan makonni kaɗan Sojojin Najeriya za su fara kai hare-haren kakkaɓe ‘yan bindiga daga cikin dazukan Zamfara.”
Discussion about this post