An bayyana cewa rashawa ce ta haddasa rashin zaman lafiya da talaucin da ake fama da shi a Afrika ta Yamma.
Babban Editan PREMIUM TIMES Musikilu Mojeed ne ya bayyana haka, kwanan nan a lokacin da ya ke jawabi wurin taron ‘Rotary Club’ na Accra, babban birnin ƙasar Ghana.
Da ya ke gabatar da jawabin sa mai take: “Satar dukiyar talakawa: Babbar masifar rashawa a Afrika ta Yamma”, ya yi matuƙar nuna damuwa cewa ƙiri-ƙiri manyan ɓarayin da ke satar kuɗaɗen Gwamnati su ne su ka haddasa talauci da rashin kwanciyar hankali da koma-bayan ƙasashen Afrika ta Yamma.
Mojeed, wanda shi ne Shugaban Cibiyar ‘Yan Jarida ta Duniya, Reshen Najeriya, ya ce idan fa ba a ɗauki matakin gaggawa a Afrika ta Yamma ba, to rashawa da cin hanci da gagarumar satar dunkiya gwamnati wadda hakkin talakawa ce, zai durƙusar da Afrika ta Yamma.
Daga nan ya yi kira ga mambobin cibiyar su ci gaba da matsa wa gwamnatoci lamba domin su daƙile satar kuɗaɗe, kamar yadda su ka tashi haiƙan su ka daƙile cutar shan-inna.
“Daƙile satar kuɗin gwamnati abu ne mai muhimmanci, saboda kwasar dukiyar talakawan da ake yi a ƙasashen Afrika ta Yamma, shi ne dalilin afkawar yankin cikin talauci, rashin kwanciyar hankali da zama koma-baya.”
Daga nan har misali ya buga da rahoton da TI ta fitar cewa Yankin Afrika ta Yamma ne mafi lalacewa wajen cin hanci da rashawa, koma-baya da raɗaɗin talauci a duniya.
Discussion about this post