Sakamakon binciken da kamfanin koyar da ilimin komfuta ‘GeyBundi’ ya gudanar ya nuna cewa sama da kashi 85% na daliban da ke kammala karatun digiri a Najeriya ba su da ƙwarewar sarrafa Komfuta.
Shugaban Kamfanin Osita Oparaugo Wanda ya sanar da haka ya ce a dalilin haka ya sa matasa da dama basa iya samun aikin yi musamman wadanda suka shafi aiki da komfuta.
Ya ce wannan matsala na daga cikin matsalolin dake sa ake samun yawan mutanen da basu da aikin yi a kasar nan.
Bayan haka Oparaugo ya ce kamfanin ta gudanar da bincike kan dalibai masu yi wa kasa hidima NYSC guda 100 kan sarrafa komfuta inda daga cikin mutum 19 ne kawai suka iya taɓuka abin azo a gani.
Ya ce binciken ya nuna cewa ilimin sarrafa komfuta da wadannan dalibai 19 ke da shi ba shi da zurfi inda abin da suka iya sun hada da iya kunawa, rubutu da aika sakonni ne kawai.
“Sakamakon binciken ya kara nuna cewa mutum 7 daga cikin 19 na da ilimin sarrafa komfuta mai zurfi amma dukan su ba su yi karatu a kasar nan ba. Mutum biyar sun Yi karatu a kasar UK, daya a kasar Amurka da daya a kasar Malaysia.
“Baya ga haka wadannan dalibai na aiki da kafafen sada zumunta da dama dake yanar gizo.
Daga nan Kamfanin ta Kuma gano cewa da dama daga cikin daliban da suka kammala karatun digiri a kasar nan na dauke da satifiket din abin da suka karanta ne kawai amma ba su fahimci abin da suka karanta ba.
“A dalilin haka ya sa matasa da dama a kasar nan basu da sana’o’in hannu.
Discussion about this post