Tun daga ranar da sojojin juyin mulki suka kifar da Gwamnatin Mohammed Bazoum a Nijar, a ranar 26 Ga Yuli, har yau mahukuntan ba su bi umarni ko guda ɗaya da ƙungiyar ECOWAS ta gindiya masu ba, duk kuwa da cewa an ƙaƙaba wa ƙasar takunkumi. Bazoum, shugaban da aka hamɓaras har yau ya na tsare shi da iyalan sa.
Fahimtar matsalar Nijar ta ƙara faɗaɗa ta yadda ake kallon yadda Amurka da Faransa su ke zaramboton shiga tsamo-tsamo wajen ‘yancin ƙasar Nijar.
A gefe ɗaya, su kuma mahukuntan sojojin mulki sun yi amfani da hankalin al’ummar ƙasar sama da miliyan 25 wajen nuna ƙiyayya Turawan mulkin mallaka, lamarin da hakan ya nuna sun shirya jan tsawon lokaci ana fafatawa da su, kafin kafin su sauka su maida mulki.
To a nan ne fa diflomasiyya za ta fuskanci ƙalubale, haka ita kan ta ECOWAS a ƙarƙashin shugaban Najeriya, Bola Tinubu da ma duniya baki ɗaya.
Jamhuriyar Nijar na ɗaya daga cikin ƙasashen da talauci ya fi yi wa katutu a duniya. Ta na sahun gaban ƙasashen da ake buga misalin irin ƙuncin rayuwar da ake fama da shi yanzu haka a duniya sanadiyyar matsalar koma-bayan tattalin arzikin da ya buwayi duniya a yanzu.
A gefe ɗaya kuma Turawan mulki na ƙasar Faransa sun tatse mafi yawan dukiyar ƙasar, to kuma har yau tun bayan samun ‘yanci, Nijar ba ta samu wani ci gaban a zo a gani ba daga hannun shugabannin da su ka riƙa mulkar ta tun 1960, in banda makwaɗaitan shugabanni masu yin birgima a kan dukiyar ƙasar, su na ƙara danna talakawan Nijar cikin ƙangin talauci.
Ana ta ruruta batun arzikin albarkatun yunaniyan a Nijar. To amma a gaskiyar magana yuraniyan ɗin Nijar fa bai wuce kashi 6 bisa 100 na yawan yuraniyan ɗin da ke duniya ba. Saboda ko a Faransa ma da ake kukan cewa ta na tatse yuraniyan ɗin Nijar, to mafi yawan wanda ta ke amfani da shi ba na Nijar ba ne, daga Kazakhstan ta ke shigo da shi.
Gaskiyar lamari Nijar ta na cikin wani yanayi, domin ba ta iya noma abincin da ƙasar ke buƙata. Kashi 1 bisa 5 na abincin da ake buƙata a Nijar duk daga waje ake shiga da shi. Dalili kenan ma ƙasar ta dogara a kan tallafin dala biliyan 2 da ta ke samu a kowace shekara.
Ya kamata sojojin mulkin Nijar su yi karatun ta-natsu, su fahimci cewa zara idanu da fankamar su fa ba za ta kai Nijar ko’ina ba, ballantana su iya fitar da ƙasar daga matsalar tattalin arzikin da ya jefa al’ummar ta cikin raɗaɗin tsadar rayuwa. Idan ba a ɗauki matakin da ya dace ba, lamarin zai iya jefa ƙasar cikin ruɗani.
Hana jiragen ruwa shiga yankin Ukaraniya da Rasha ya yi, ya haddasa tsakon samun tallafin abincin da Majalisar Ɗinkin Duniya ke saye daga Ukaraniya ya na bai wa Afrika, wanda zuwa shekara mai zuwa aka tsara yawan wanda Afrika ke samu zai ƙarasa kaiwa Yuro miliyan 500. Saboda haka Nijar na buƙatar wannan tallafi, haka ta na buƙatar tallafin Dala miliyan 153 na litattafai daga Amurka a wannan shekara. Idan ba haka ba kuwa, to ƙasar za ta ƙara shiga ruɗanin ƙuncin rayuwa, wanda talakawa kaɗai zai shafa.
Ya kamata sojojin mulkin Nijar su yi la’akari da wannan mawuyacin hali da ƙasar ke ciki, da kuma wanda za su ƙara jefa ƙasar a yanzu.
PREMIUM TIMES na kira ga ECOWAS da Shugabannin Ƙasashen ECOWAS cewa su ci gaba da zurfafa bin turbar diflomasiyya domin sulhunta rikicin shugabancin Nijar. Kada takunkumin da aka ƙaƙaba wa ƙasar a yanzu ya toshe hanyar iya farfaɗo da ƙasar bayan mulkin Tchiani.
Misali, yanke wutar lantarki da aka yi a Nijar zai ƙara gurgunta tattalin arzikin ƙasar, wanda dama shure-shuren mutuwa tattalin arzikin ke yi.
Kada a tsaya ana kafa hujja da gutsiri-tsomar zargin salwantar dala miliyan 153 na sayen makamai a matsayin hujjar halasta juyin mulki a Nijar.
Tabbas cin hanci da rashawa abu ne da ya haifar da kasa ci gaban Nijar tun bayan samun ‘yanci. To kuma ba juyin mulkin su Tchiani ke farko ba, wajen kafa hujja da cin hanci da rashawa a matsayin dalilin kifar da gwamnatin dimokraɗiyya.
Amma kuma wannan zargin salwantar kuɗaɗen makamai har dala miliyan 153, tilas a binciki yadda aka yi da kuɗaɗen.
Kada a manta, tun shekaru uku da su ka wuce PREMIUM TIMES ta bada labarin wannan harƙallar salwantar dala miliyan 153 ta sayen makamai.
Don haka zai yi kyau a ga yadda za ta ƙarke tsakanin tsohon Shugaban Ƙasa Mahammoudou Issoufou da kuma Tchiani, wanda a baya ya yi aiki ƙarƙashin gwamnatin Issoufou, gwamnatin da kuɗaɗen su ka salwanta a ƙarƙashin ta.
A na ta ɓangaren, bai yiwuwa Faransa ta riƙa amfani da wata yarjejeniyar gare da ya tsara fiye da shekaru 60, ya na amfani da ita, ta na yin kane-kane cikin sha’anin ƙarar da ta karɓi ‘yancin kai tun tun 1960.
Dama kuma yarjejeniya ce da ƙarara ke nuna cewa Faransa ɗin ce ke tatsar ƙasar da duk ta raina.
Faransa, ƙasar da ta tara shugabannin duniya a cikin watan Yuni domin shata sabuwar alƙiblar cin moriyar juna, bai kamata kuma a ce ita ke yin riƙo da wata tsohuwar yarjejeniyar da ta naniƙe wa ƙasashen da ta mulka ba. Ta ƙyale su hakanan su samar wa kan su mafita.
Babban kuskure ne ‘yan Nijar da irin su Mali da Burkina Faso su riƙa kallon cewa mutanen da ke sanye da khaki ne za su ceto su daga matsalolin su.
Shi kan sa Tchiani na Nijar ai tun cikin 2011 ya ke Shugaban Zaratan Sojojin Tsaron Fadar Shugaban Ƙasa. Ashe kenan duk wata matsala da sojoji su ka haifar, ya na daga ciki kenan.
Don haka batun cewa ya ƙwace mulki ne don ya ceto ƙasar, abin shakku ne. PREMIUM TIMES na yin kira gare shi ya katse gugumarar neman goyon bayan da ya ke yi a Yamai, ya bayyana lokacin maida mulki ga zaɓaɓɓiyar gwamnatin dimokraɗiyya.
Kuma wannan matsaya ce ECOWAS da Najeriya da Najeriya su ka ɗauka. Najeriya na fuskantar ƙalubale, domin abin da ya shafi Nijar ya shafe ta, kasancewa al’ummar Hausawa da Fulani na Arewacin Najeriya kisan ‘yan’uwan juna su ke da na Nijar.
A ɗaya gefen kuma abin da ke faruwa a yanzu da waɗanda su ka faru a baya, sun nuna kakaf a ECOWAS babu wata ƙasa da ke da ƙarfin sojan da ke iya daƙile matsalar tsaro a cikin ta.
Saboda haka su ma Sojojin Najeriya ba su da wani shiri na tattago wani yaƙi har cikin wata ƙasa a yanzu.
A yanzu an watsa sojojin Najeriya su na aikin tsaro a jihohi 34 cikin 36 na ƙasar nan. Ga shi ƙarara Boko Haram ‘yan ISWAP sun sake dannowa, ga dandazon ‘yan gudun hijira a kan iyakoki, ga kuma dandazon ‘yan bindiga. To da me za a ji?
Ƙarara dai ‘yan Najeriya sun nuna cewa ba su son a karkashe ‘yan’uwan su ‘yan Nijar haka kawai ba gaira ba dalili.
Saboda haka, PREMIUM TIMES na kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a cikin Najeriya da ƙasashen duniya su ci gaba da matsin-lambar yin sulhu a cikin ruwan sanyi. Amma afka wa Nijar da yaƙi ba alheri ba ne.
Discussion about this post