• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    TSUMAGIYAR KAN HANYA: An umarci ‘yan sandan Abuja su riƙa binciken motar ko wa kuma ko ɗan wa

    Kotu ta daure magidancin da ya guntile hannun abokinsa kan zargin lalata da matarsa

    Jami’an Kwastam sun kama haramtattun kaya na miliyoyin naira a Katsina

    Hukumar Kwastam ta kama haramtattun kaya na naira biliyan 6.6 a jihar Ogun

    American University of Nigeria Student -Crt- Google

    Malaman jami’o’i na roƙon a biya su albashin wata da watannin da aka riƙe masu

    ‘Yan sanda sun damke faston da ake zargin yayi wa ‘yar shekara 19 fyade

    Kotu ta yanke wa mahaifin da ya yi shekara 9 yana lalata da ƴa’ƴan sa mata biyu

    Ƴan sanda sun kama magidancin da ya yi wa matar makwabcinsa fyade

    ABUJA: Kotu ta daure wasu ‘yan mata biyu saboda yawon gulmace-gulmace a unguwa

    Kotu ta tsare matar da aka kama tana madigo da ‘yar shekara 8 a Kaduna

    Mahukunta a Abuja sun kama ƴan iskan gari mutum 400 da motoci 50 da suka karya doka

    Tinubu ya naɗa tsohon ministan Abuja, Modibbo, Kakanda, Baba-Ahmed mashawarta a ofishin mataimakin shugaban kasa

    ‘Yan sanda sun kama tsohon da ya yi wa ‘yar shekara hudu fyade a Katsina

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    DARAJAR ƘWALLON ƘAFA TA KOMA SAUDIYA: Karim Benzema zai riƙa ɗaukar albashin kusan Naira Biliyan 100 a shekara, a ƙungiyar Al-Ittihad

    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

    QATAR 2022: Ko ƙasashen Afrika za su fidda nahiyar jin kunya a duniyar ‘yan ƙwallo

    DAGARGAZA ARGENTINA: Ƙasar Saudiyya ta ba da hutun kwana Ɗaya a wataya

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    BIDIYO: Yadda rufe iyakar Najeriya da Nijar, ya jefa mu cikin tsananin fatara, da halin kakanikayi a yankin Katsina – Saidu

    Yadda SSS da Jami’an Gidan Kurkuku suka kwashi ‘yan kallo a kotu, saboda Emefiele

    BIDIYO: ‘Duk wanda ya ci kuɗin Tallafin Korona a Jigawa sai ya amayo shi’ – Gwamna Namadi

    BIDIYO: ALhazan Kano sun gama shiri tsaf don ‘Hawan Arafat’ – Alhussain Maiwada

    JERIN SUNAYE: Jami’o’i 51 da ba za su dauki dalibin da ya ci kasa da maki 180 a jarabawar JAMB ba

    TSARIN BAI WA ƊALIBAI RAMCE: Abubuwan da suka wajaba ɗalibai da iyaye su sani

    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

No Result
View All Result

RA’AYIN PREMIUM TIMES: Rashin cancantar yi wa ‘Yan Majalisa watandar mahaukatan kuɗaɗe, lokacin raɗaɗin tsadar rayuwa

Premium Times HausabyPremium Times Hausa
August 2, 2023
in Labarai
0
RA’AYIN PREMIUM TIMES: Rashin cancantar yi wa ‘Yan Majalisa watandar mahaukatan kuɗaɗe, lokacin raɗaɗin tsadar rayuwa

Yayin da talakawan Najeriya ke cikin halin raɗaɗin tsadar rayuwar da rashin kyakkyawan shugabanci ya haddasa masu, su kuwa ‘Yan Majalisa sun nuna babu ruwan su da mawuyacin halin da al’ummar da su ka zaɓe su ke ciki.

Abin da kawai ke gaban su shi ne yadda za su yi rayuwar jin daɗi su da iyalan su a Abuja, a wannan lokacin da kowa ya shiga taitayin sa, saboda raɗaɗin ƙuncin rayuwa.

Ƙiri-ƙiri ko kunyar talakawa ba su ji, sun ware wa kan su jimillar Naira biliyan 110, don sayen kayayyakin more jin daɗin rayuwa a Abuja. Sauran talakawa da marasa galihu kuma sama da miliyan 100 an bar masu Naira biliyan 500. Kuma a cikin su ko mutum goma ba zai amfana da tallafin ba.

Za a sai wa ‘yan majalisa zunduma-zunduman motoci masu sulken hana harsashi ratsawa cikin motar. Su kuma talakawa an bar su a hannun ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda su na kisa, ba ƙaƙƙautawa.

‘Yan Majalisar Tarayya sun ajiye rigar kunya a gefe, sun nemi a yi masu ƙarin albashi da alawus-alawus, saboda wai rayuwa ta yi tsada a yanzu.

Amma kuma har yanzu ana ta kwan-gaba-kwan-baya kan batun ƙara wa ma’aikata albashi.

Saboda haka wannan rashin mutunci da rashin tausayin talakawa ne a ce masu wakiltar marasa galihu su riƙa kamfatar mahaukatan kuɗaɗe don su ji daɗin rayuwar su, musamman a lokacin da talakawa ke cikin tsananin tsadar rayuwa.

Hakan da su ka yi ya nuna cewa tun ba a je ko’ina ba, ba kishin jama’ar da ya zaɓe su ne a gaban su ba. Hakan da su ka yi ya daɗa janyo masu baƙin jini da tsana daga cikin talakawa.

Jama’a ku dubi yadda wasu ‘yan majalisar da su ka sauka su ka sace komai daga ofishin su. Hatta talabijin da darduma ba su bari ba. Wannan abin kunya ce tabbas. Kuma abin takaici har yau babu wani hoɓɓasan da aka yi domin a dawo da kayan. Tir, girma dai ya faɗi.

Ko ma dai me za a ce, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya fara saƙa da mugun zare.

Sabon salon tsarin mulkin Shugaba Bola Tinubu a cikin wata biyu kacal ya gigita ‘yan Najeriya. Cire tallafin fetur da sakin Naira a cikin kasuwa ba tare da makiyayi ba, ya haifar da tsadar rayuwa da tsadar kayan abinci zuwa kashi 22.7%.

Rabon da a fuskanci irin wannan balbalin tsadar farashin kayan masarufi da na abinci kuwa, tun cikin 2005.

Kuɗin zirga-zirga a motocin sufuri ya ƙaru. Mutane da dama sun gwammace su riƙa tafiya a ƙasa. Wasu sun ajiye aiki, saboda albashin su ba zai iya biyan kuɗin motar da su ke kashewa zuwa ofis ba.

Abinci ya yi tsada a birane da ƙauyuka. Cefane ya gagari magidanta da dama, saboda ɗan abin da su ke samu ba ya isar su. Waɗanda ambaliyar ruwa ta janyo wa mummunar asara tun 2022, har yau gwamnatin tarayya ba ta cika alƙawarin da ta masu ba.

Karatu a makarantun jami’o’in ƙasar nan na neman ya gagari ‘ya’yan talakawa, domin a wasu makarantun ƙarin kuɗin makaranta ga ɗalibai ya kai Naira 256,000.

Sai ga shi duk da irin wannan mawuyacin hali da ake ciki, su kuma ‘yan majalisa hankalin su ya fi karkata ga abin da za su samu su ji daɗin more rayuwar su.

Don haka shawarar da za mu bai wa ‘yan majalisa ita ce su kwaikwayi na wata ƙasa, ko wasu ƙasashen da kwata-kwata ba su ma kama ƙafar da za a kwatanta ƙarfin tattalin arzikin su da na Najeriya ba.

Sannan kuma kada Shugaban Majalisar Wakilai ta Ƙasa Yusuf Abbas kada ya ƙara yawan kwamitocin majalisa daga 110 da ya taras, zuwa 134 da ya ke son kafawa.

‘Yan Najeriya fa sun gaji da wannan bulkara da ragabzar kuɗaɗe da ake yi a kan idon su. Ido ai mudu ne. Idan bai san kunya ba, to ya san kima.

Tags: MajalisaPremiumTimeTimesWatanda
Previous Post

SHARI’AR ZAƁEN 2023: Shari’a tsakanin Atiku da Tinubu ta ƙare, saura bayyana ranar yanke hukunci – Inji kotu

Next Post

JUYIN MULKIN NIJAR: Rasha ta ce ba ta goyon bayan masu ƙumajin afka wa Nijar da yaƙi

Premium Times Hausa

Premium Times Hausa

Next Post
Kasar Rasha fitar da rigakafin Korona na farko a Duniya

JUYIN MULKIN NIJAR: Rasha ta ce ba ta goyon bayan masu ƙumajin afka wa Nijar da yaƙi

Discussion about this post

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • MACE MAI KAMAR MAZA: Yadda Falmata ta kutsa cikin sana’ar gyarar waya ta yi zarra
  • Tinubu ya umarci jami’an tsaro su yi ƙumumuwa, su ceto ɗaliban Jami’ar Zamfara daga hannun ‘yan bindiga
  • Kwararrun likitocin hakora 84 kacal ake da su a Najeriya – NAPD
  • SHUGABANCIN APC: Ko biyayyar da Ganduje ke wa Tinubu za ta sa ya yi kargo a ɗigirgiren shugabancin APC?
  • SAKAMAKON AMBALIYA: Yadda yunwa ke nuƙurƙusa da kisan talakawa a yankunan Arewa

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.