Tun cikin 2007 aka fara kiki-kaka a kan batun kuɗaɗen fanshon da tsoffin gwamnoni ke karɓa, a bayan saukar su daga mulki har ƙarshen rayuwar su.
Wannan karɓar kuɗaɗen da su ke yi kuwa, babban laifin karya Dokar Najeriya ce. Abin da ma ya ƙara wa laifin muni a yanzu, akwai kamar tsoffin gwamnoni bakwai ko takwas a cikin ministocin gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, waɗanda za su ci gaba da karɓar wannan haramtacciyar garaɓasa, kuma duk a lokaci guda su riƙa karɓar albashi a matsayin su na ministoci.
Ƙarin abin takaicin ma shugaban ƙasa na cikin gungun waɗanda ke karɓar fansho ɗin, kuma ga albashin sa na shugaban ƙasa ya na karɓa. Saboda ya yi Gwamna a Jihar Legas daga 1999 zuwa 2007.
Gwamnatin Jihar Legas ta wancan lokacin a ƙarƙashin Bola Tinubu ce ta fara ƙirƙiro tsarin riƙa bai wa tsoffin gwamnoni kuɗaɗen fansho. A yau fiye da rabin jihohi 36 su na bin wannan haramtaccen tsarin.
Ya kamata Shugaban Ƙasa ya daina karɓar kuɗaɗen fanshon tsoffin gwamnoni, kuma hakan ya zama darasin da ministocin sa da su ka taɓa yin gwamna za su koya a wurin sa.
Tantagaryar rashin adalci ne a ce Gwamna ya kammala wa’adin sa, ya tafi ba tare da biyan ‘yan fansho haƙƙin su ba, ga rashin aikin yi a jihar sa, kuma ga raɗaɗin talauci, amma ya koma shi ya na karɓar fansho, sannan kuma ya riƙa karɓar albashi duk a lokaci guda, idan aka naɗa shi minista.
SERAP ta yi daidai yayin da kwanan nan ta yi kira ga waɗannan tsoffin gwamnoni su daina karɓar fansho. Sannan kuma ta jawo hankalin Shugaban Ƙasa ya dakatar da wannan harƙalla.
Ministocin da yanzu haka za su ci gaba da karɓar wannan haramtacciyar garaɓasa, sun haɗa da: Nyesom Wike, Adegboyega Oyetola, Atiku Bagudu, David Umahi, Ibrahim Geidam, Simon Lalong. Amma shi Bello Matawalle ba ya ciki, domin shi ne a cikin 2019 ya haddasa Majalisar Dokokin Zamfara ta soke Dokar Bada Fansho Ga Tsoffin Gwamnoni.
To wasu jihohi sun soke wannan doka, wasu kuma sun yi biris da ita. Akwai kuma wasu tsoffin gwamnonin wasu jihohi da su ka ƙi karɓar waɗannan haramtattun kuɗaɗen fansho.
Haramcin waɗannan kuɗaɗe da tsoffin gwamnoni ke karɓa a matsayin fansho, ya fito fili a cikin kundin dokokin Najeriya.
“Dokar Najeriya ta ce sai wanda ya yi wa gwamnati aiki daga shekara 10 abin da ya yi sama za a kira ɗan fansho. Amma kuma saboda tantagaryar rashin tausayin talaka, tsoffin gwamnonin da ke karɓar fanshon shekaru huɗu ko takwas su ka yi a kan mulki.
Jihar Legas ce ta fara fito da wannan gadangarƙamar a cikin 2007, inda ta amince za ta riƙa bai wa tsohon Gwamna kuɗaɗen fansho Naira miliyan 30 a kowace shekara. Kuma za a ba shi gida a Legas da Abuja, amma idan ya yi shekaru takwas ya na mulki. A sake masa sabbin motocin shiga guda shida a duk bayan shekaru uku.
Sannan za shi da iyalan sa za’a ɗauki nauyin kula da lafiyar su. Kuma a ba su masu yi masu hidima a gidajen su.
Jihohin Akwa da Gombe tun bayan Dokar 2007 su na ta gaganiyar biyan Naira miliyan 300 da miliyan 200 a matsayin waɗannan haramtattun kuɗaɗen fansho.
Ya zuwa 2017, jihohi 21 sun kwashi jimillar Naira biliyan 37.4 sun ɗibga wa tsoffin gwamnoni a matsayin kuɗaɗen fansho ga tsoffin gwamnoni 47.
Ya kamata gwamnatin Bola Tinubu ta kawo ƙarshen wannan taƙadaranci, ganin yadda marasa galihu ke ta haƙilon raɗadin tsadar rayuwa bayan cire tallafin fetur.
Sannan bai kamata gwamnati ta ɗaure gindi ana kwasar maƙudan kuɗaɗe ana jibga wa wasu ‘yan tsiraru ba, musamman yanzu a lokacin da ƙasa da al’ummar cikin ta ke cikin mawuyacin hali.
Discussion about this post