Abin da ya faru kwanan baya a jihar Adamawa, inda mutanen gari, musamman matasa suka riƙa ɓarke rumbunan ajiyar kayan abincin tallafi da kantinan ‘yan kasuwa, su na jidar abinci, kayan masarufi da sauran kayayyaki, babbar hujja ce mai tabbatar da cewa guguwar yunwar da ta darkako cikin Najeriya, tuni har ma ta rigaya ta shigo.
Dama akwai jidalin ƙuncin rayuwa, to kuma sai aka ƙarasa kwantar da marasa galihu a ƙasa, ta hanyar cire tallafin fetur, ba zato ba tsammani.
Wannan abu da matasa su ka aikata, wani saƙo ne fa muhimmi suka aika wa gwamnati cewa sun fa gaji da kwana da tashi a cikin yunwa haka nan.
Wannan lamarin da ya faru, ya nuna cewa akwai buƙatar jami’an tsaro su ƙara kula da sa-ido sosai a sauran jihohi 36 na ƙasar nan. Saboda gudun kada abin ya bazu cikin sauran jihohi.
Dama irin haka ta taɓa faruwa a lokacin zaman kullen korona, cikin 2020.
A hargitsin kwasar ‘ganimar’ Adamawa dai har mutum huɗu aka kashe, a ƙoƙarin da ‘yan sanda su ka yi na tarwatsa masu kwasar kayan abinci.
Ita da kan ta Mataimakiyar Gwamnan Adamawa, Kaletapawa Farauta, ta yarda da bakin ta cewa, “lallai jama’a na fama da yunwa a ƙasar nan, kuma su na cikin wahala.”
Yunwa bala’i ce, domin ta na haddasa jama’a yin tunziri a faɗin duniya, lamarin da kan haifar da juyin-juya-hali ko kuma juyin-turu. Hakan ta faru a ƙasashe da dama.
Lamarin da ya faru a Jihar Adamawa ya nuna cewa akwai fa gagarimar matsalar yunwa a ƙasar nan. Amma sakacin jami’an gwamnati ya sa su ka ƙi ɗaukar darasi tun a kan abin da ya faru a Jihar Taraba, mako biyu kafin faruwar irin sa ɗin a Adamawa, inda aka fara rumbun ajiyar abinci mallakin tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Sardauna, aka yi masa ƙarƙaf.
A halin yanzu a ƙasar nan, lamarin raɗaɗin tsadar rayuwa ya yi tsananin da kowa ta kan sa ya ke yi. Buhun shinkafar da ake sayarwa Naira 27,000 kafin watan Mayu, a yanzu bayan cire tallafin fetur ya kai Naira 46,000, a wasu garuruwan ma har Naira 50,000.
Sannan kuma duk wani kayan abinci, masarufi da kayan cefanen miya sun ƙara farashi. Shi kuwa farashin zirga-zirga a kan ababen hawa abin babu ko daɗin ji. A wasu garuruwa ya nunka sau uku. Babban misali shi ne yadda a yanzu daga Legas zuwa jihohin Kudu maso Gabas, sai fasinja ya biya Naira 30,000. Amma kafin a cire tallafin fetur Naira 10,000 ake biya. Ga shi kuma albashi na nan tsaye cak bai ƙaru ba a ma’aikatun gwamnati. A ma’aikatu masu zaman kan su kuwa, sai zabge ma’aikata ake yi ana korar da yawa daga aiki.
Yayin da gwamnatin Tinubu ta daburce, ta gigice, tsakanin buƙatar ma’aikata ta ƙarin albashi da kuma ƙarancin kuɗaɗen shiga a jihohi, to abin da matasa su ka yi a Taraba da Adamawa ya na nuna akwai fa gagarimar masifar yunwa a ƙasar nan, wadda talakawa da marasa galihu ba za su iya jure wa raɗaɗin ta ba.
Gwamnatin Tarayya da kan ta ta san illar tsadar rayuwar da jama’a su ka afka sanadiyyar tsauraran matakan tattalin arzikin da ta ɗauka. Saboda ta san ana cikin wahala ne ma har ta ce za ta raba metrik tan 250,000 na kayan abinci da takin zamani ga mutane miliyan 50.
A yankunan karkara da yawan gaske ‘yan bindiga da Boko Haram sun hana manoma zuwa gona. Bi kawai su ke yi su na kashe manoma da sauran mutanen karkara, duk kuwa da cewa an canja manyan hafsoshin tsaro, har yau ba a ga wani ci gaba ba.
Idan ba a samu ci gaban zaman lafiya a karkara ba, to mafarkin wannan gwamnatin na samar da hekta 500,000 domin bunƙasa noma, zai zama almara ce kawai.
Ko shakka babu, Shugaba Tinubu ya yi azarɓaɓi, giringiɗishi da giribtun cire tallafin fetur da sakin Naira a tsakiyar kasuwa ta ciyar da kan ta abinci, ba tare da makiyayi ba.
To ga shi nan yanzu lamarin ya na neman ya gagari gwamnati ta shawo kan sa. Ana haka kuma an afka cikin rikicin ƙarin albashi tsakanin gwamnati da ma’aikata.
A jawabin Tinubu cikin makon da ya gabata, ya shaida wa ‘yan Najeriya cewa ya na sane da irin mawuyacin halin da su ke ciki na tsadar rayuwa. Sai dai kuma bilumbituwar da gwamnati ke yi kan tsare-tsaren tattalin arziki sun nuna babu wata alamar sauƙi nan gaba, sai ma ci gaban mai ginin rijiyar da ke yi a kowace rana.
Yayin da mu ke cikin halin ƙaƙanikayi saboda karyewar darajar Naira, sakamakon fama da ƙarancin dala, a gefe ɗaya kuma ga biliyoyin dalolin Najeriya can a hannun gurzagullan ƙartin barayin fetur masu sanye da rigar gwamnati da kuma manyan kamfanoni, an kasa ƙwatowa.
Idan aka tatsi ruwan cikin su, za a iya samun kuɗaɗen shiga limamin sama da dala biliyan 150. Ƙwato waɗannan maƙudan kuɗaɗen zai ɗaga darajar Naira, kuma ya inganta rayuwar ‘yan Najeriya.
Amma abin takaici, an bar asusun ajiyar rarar dukiyar Najeriya na waje da dala biliyan 34 kacal a cikin sa.
Gwamnatin Buhari ta kauda kai daga ƙwato waɗannan maƙudan, lamarin da ya kai mu afkawa cikin wannan mummunan yanayin da ƙasa ke ciki.
Saboda haka babban laifi ne ƙarara idan ita ma Gwamnatin Tinubu ta ɓuge, ta kasa ƙwato kuɗaɗen, kamar yadda gwamnatin Buhari ta yi biris da su.
Babban Lauya Femi Falana dai ya rubuta wa Shugaba Tinubu wasiƙa cewa, “Ba fa daidai ba ne manyan ɓarayin gwamnati su tafka laifi, sai ka ƙyale su ka koma ka na dukan talakawan da ba su ne su ka yi laifin ba.”
Akwai gagarimar matsala fa a Najeriya. Kashi 53 bisa 100 na matasan Najeriya ba su da aikin yi. Najeriya ce ta biyu a yawan wannan adadi a duniya.
Bai kamata a wannan yanayi a ƙara fito da wasu hanyoyin taɓargaza da almubazzaranci da kuɗaɗen gwamnati ba, ta hanyar naɗa ministoci har 48, fiye da 36 ɗin da dokar ƙasa ta ƙayyade.
Ga kuma ƙarin albashi da alawus da kuɗaɗen ɓalle-bushashar rayuwa mai tsadar da ‘yan Majalisa ke neman a ƙara masu.
Mu na kira ga Shugaba Bola Tinubu da Gwamnoni 36 na jihohin ƙasar nan cewa, su guji tunzirin talakan da raɗaɗin yunwa da tsadar rayuwa ta kai shi bango har ya kai ga ya hasala.
Discussion about this post