Ƙididdigar da wata cibiyar kasuwanci a hanyoyin zamani, mai suna Picodi ta fitar, ta nuna cewa akasarin kowane magidanci a Najeriya ya na kashe kashi 59 bisa 100 na kuɗaɗen da ya ke samu wajen sayen abinci.
Yawancin masu yin sana’o’in hannu na gargajiya ko na zamani, har ma da masu kasuwanci, duk matsin tattalin arziki da raɗaɗin tsadar rayuwa ya sa sun shiga taitayin su, kamar dai yadda wata mata tela, mai shagon kayan ‘yan ƙwalisa ta tsinci kan ta a Kano, a yanzu haka.
“A gaskiya ina jin jiki. Ba na iya biyan buƙatun yau da kullum na gida na, musamman abincin da za mu ci. Farashin komai ya cilla sama, tilas na rage cin nama, ƙwai da sauran kayan gina jiki.” Inji A’isha Ibrahim, bazawara mai riƙe da ‘ya’yan ta uku.
Irin rayuwar da A’isha Ibrahim ke yi, kusan irin ya ce miliyoyin mutane ke yi a Najeriya, ƙasar da ta fi sauran ƙasashen Afrika yawan jama’a.
Farashin kayan abinci sai ƙara hauhawa ya ke yi, a gefe ɗaya kuma samu na ƙara rayuwa, riba kuma ta na ƙara ƙaranci.
A bayanan ƙididdigar da Picodi ta fitar a cikin Agusta, ya nuna ɗan Najeriya ya na kashe kashi 59 na abin da ya samu wajen sayen kayan abinci. Haka binciken da su ka yi ya nuna cewa ɗan Najeriya ne ya fi kashe abin da yake samu wajen sayen kayan abinci. Bincike a ƙasashe 105 ya nuna haka.
A cikin ƙasashen 105, Najeriya ce ta zo ta ɗaya wajen kashe kuɗaɗen da magidanci ke samu a sayen abinci.
‘Yan Najeriya sun fi ‘yan Bangaladish kashe kuɗaɗen da su ke samu wajen sayen kayan abinci. Sun fi ‘yan Kenya, sun fi ‘yan Myanmar, kuma sun fi ‘yan Laos.
Amma ‘yan ƙasashen Amurka, Singapore, Birtaniya, Ireland da Switzerland, su abin da su ke kashewa kan abinci bai ma kai kashi 10 bisa 100 na abin da su ke samu ba.
Ba’Amurke ya na kashe kashi 6.7 bisa 100 na abin da ke shigowa aljihun sa wajen sayen kayan abinci da lemun kwalba da na kwali, ɗan Birtaniya na kashe kashi 8.7 bisa 100, ɗan Singapore kashi 8.4 bisa 100. Ɗan Najeriya kuwa ya na kashe kashi 59 bisa 100.
Rahoton Picodi ya ce aƙalla tantirin talaka a Najeriya zai buƙaci kashe Naira 48,200 wajen abinci duk wata. Alhali kuwa mafi ƙanƙantar albashi a Najeriya Naira 30,000 ce.
‘Yan Najeriya sun ƙara afkawa cikin raɗaɗin tsadar rayuwa, tun bayan sa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya cire tallafin fetur, a ranar 29 Mayu, a wurin rantsar da shi.
Discussion about this post