Malejin tsadar rayuwa ya ƙara cillawa sama sosai, yayin da tsadar abinci ta buwayi ‘yan Najeriya a kowane yankin faɗin ƙasar.
Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa, NBS, ta bayyana cewa farashin kayan abinci ya cilla sama zuwa kashi 26.98 a cikin watan Yuli, idan aka kwatanta da yadda ya ke a kashi 25.25 a cikin watan Yuni.
NBS wadda hukumar Gwamnatin Tarayya ce, ta ƙara da cewa idan aka koma nazarin tsadar abinci a wannan shekara har aka kwatanta da shekarar 2022, za a ga cewa an samu ƙarin tsadar abinci da kashi 4.44 a Yuli 2023, idan aka auna tsadar da Yuli 2022, inda a wancan lokacin malejin tsadar abinci ya tsaya a 19.64.
Rahoton ya ce a Yuni 2023 farashin tsadar abinci ya tsaya daidai kashi 25.25, amma kuma a Yuli 2023 ya cilla zuwa kashi kashi 26.98, tun watan bai wuce tsakiya ba.
Hakan ya na nuni da cewa ba a ma san iyar inda malejin tsadar rayuwa zai dangwale ba, daga nan zuwa ƙarshen Yuli.
Tuni dai hukumomi na ta yin gargaɗin cewa miliyoyin jama’a za su shiga cikin ƙuncin rayuwa, saboda matsalar kayan abinci da za a fuskanta a wasu ƙasashe da yankunan su, ciki kuwa har da Arewacin Najeriya.
A gefe ɗaya kuma ana ganin cewa matsawar yaƙi ya ɓarke idan Sojojin ECOWAS su ka kai wa Nijar hari, to yankin Sahel baki ɗaya, ciki har da Arewacin Najeriya zai afka cikin matsalar ƙarancin abinci.
Tsadar kayan abinci dai ta ƙara tsanani tun bayan cire tallafin fetur.
Alƙawarin raba kayan tallafi da samar da yaƙin zamani mai rangwame kuma har yanzu talakawa sun zuba ido.
Discussion about this post