Shugaban jami’ar Bayero ta Kano Sagir Abbas, ya sanar da wasu muhimman tsare-tsare da tallafi da jami’ar ta samar domin ma’aikatanta da malamai.
Abbas ya ce jami’ar ta hada hannu da bankin al’umma dake jami’ar domin baiwa ma’aikata dake da ƴaƴa a makarantar bashin kuɗin makarantar ƴaƴan su, su biya cikin watanni shida.
” Wasu daga cikin malaman mu na da yaya a jami’ar, saboda haka muka tsara yadda za su amshi rancen kudin makarantar ƴaƴan su, su biya a hankali, yayin da jami’ar za ta biya kudin ruwan da bankin za ta caja.
” Bayan haka mun samar da abinci domin rabawa malamai da kungiyoyi a makarantar, suma za a bada su bashi mutane su rika biya a hankali
” Haka kuma jami’ar ta siya manyan motoci na ɗaukar ma’aikata daga gidajen su zuwa jami’ar da mayar da su gida idan aka tashi aiki.
Abbas ya kara da cewa an siya kekunan hawa domin kananan ma’aikata da ke bukata. Za a basu bashi kan naira 50,000 su biya cikin wata shida ga duk mai bukata.
A karshe Abbas ya ce duka wannan tsare-tsare an yi su ne domin malamai da ma’aikata su samu sauki a wajen aiki da rage raɗaɗin rayuwa da ake fama da shi a kasar nan.
Discussion about this post