Gwamna Umar Dikko-Radda na Jihar Katsina ya ba da umarnin raba shinkafa buhu 40,000 ga mutanen jihar don rage raɗaɗin rayuwa da mutane ke fama da shi tun bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi a watan Mayu.
Wata sanarwa da ya saka a shafin sa na sada zumunta, Gwamna Raɗɗa ya ce gwamnatinsa ta sayo shinkafar ne daga kuɗin rage raɗaɗi da jihar ta samu daga gwamnatin tarayya da aka raba wa jihohin kasar nan
Bayan haka za a kafa kwamitoci wanda za su raba shinkafar ga mabukata da talakawa a duka kananan hukumomin jihar.
Sannan kuma ya gargaɗi waɗanda aka dora wa alhakin raba shinkafar da su tabbata an yi rabo cikin adalci ba tare da an yi zamba ko kuma wasu sun yi sama da faɗi da abincin wajen rabo ba.
Ya kara da cewa gwamnati za ta sa ido akan yadda za a ayi rabon kuma duk wanda aka samu yana na aikata ba daidai ba zai ɗanɗana kuɗar sa.
Discussion about this post