Gwamnatin Kaduna tare da hadin gwiwar kungiyar jin kai ta kasar Qatar, wato Qatar Charity Foundation sun kaddamar da aikin ginin gidaje 500,000 ga marasa galihu, miskinai da talakawan jihar Kaduna.
A lokacin bikin aza tubalin soma ginin gwamnan jihar Uba Sani ya yaba matuka ga ofishin jakadancin Qatar dake Najeriya saboda zabar Kaduna a matsayin daya daga cikin jihohin da za su ci gajiyar ayyukan jin kai da kasar ke gudanarwa a Najeriya da sassan duniya.
Gwamna Sani ya ci gaba da cewa aikin ginin gidajen na daya daga cikin muhimman burikan gwamnatin jihar shekaru da dadewa karkashin shirinta na samarwa masu karamin karfin muhallin da za su rika zama cikin kwanciyar hankali.
“Za su tabbatar da ganin sun samu marayu sama da dubu daya da za a ba su tallafi domin su yi karatu, haka kuma za su bayar da kayan sana’a ga mutane sama da dubu biyar.”
Ba a nan kawai za a tsaya ba, hatta gajiyayyu, da waɗanda ke fama da tsananin talauci duk za su amfana da wannan aikin taimako.
A na sa jawabin, jakadan Qatar a Najeriya Dr. Ali Bin Ghanem Al-Hajri ya ce, kasar za ta kashe miliyoyin daloli wajen gudanar da wannan aiki.
“Sannan kuma za a raba kayan ayyukan sana’o’in hannu kamar injunan walda, kekunan dinki, kayan aski da na gyaran gashin mata, sanan kuma za a gina daruruwan rijiyoyin burtsatsai a kananan hukumomi 23 dake jihar Kaduna.
Wasu mazauna Kaduna da suka tattauna da PREMIUM TIMES HAUSA, a garin Kaduna, sun ce wannan abu ne mai matukar mahimmanci musamman a wannan lokaci da mutane ke fama da kan su.
” Ace yau za a gina matsakaitan gidaje don Talakawan Kaduna abu ne mai matukar amfani sannan kuma da jinjina wa gwamna Uba Sani
” Baya ga wannan abu da za su yi, akwai kuma tallafi masu yawan gaske da za su rabawa mutanen Kaduna. Fatan mu shine Allah ya sa a wanye lafiya, sannan wanda aka yi domin su abin ya kai gare su.
Discussion about this post