Kungiyar kwadago reshen jihar Kaduna ta yi kira gwamnati cewa ma’aikatan gwamnati a jihar na bukatar a fara biyan su da naira 200,000 a matsayin mafi kankantan albashi da sa ran cewa zuwa shekarar 2024 albashin ya iya karuwa zuwa naira 500,000 a wata.
Shugaban kungiyar Ayuba Sulaiman ya sanar da haka ranar Laraba yayin da kungiyar suka gudanar da zanga-zangar nuna adawar su da cire tallafin man fetur da gwamnati ta yi.
“Za mu so gwamnati ta fara biyan mu albashi daga naira 200,000 in ya so cikin farkon shekarar 2024 gwamnati ta kara albashin zuwa naira 500,000.
Kungiyar ta ce abinda ya fi dacewa shine a dawo da kudin litar mai naira 187.
Kungiyar kwadago ta kasa ta gudanar da zanga-zangar nuna kin amincewa da janye tallafin mai da gwamnatin Tinubu ta yi tun Bayan rantsar da sabuwar gwamnatin.
Tinubu ya ce gwamnatin sa za ta kawo karshen tsananin wahalar da ƴan Najeriya suka afka ciki dalilin haka.
Discussion about this post