Gwamnatin mulkin soji na Nijar ta yanke hulɗa da Najeriya da Togo da Amurka da Faransa.
Hakan na kunshe ne a jawabi da shugaban mulkin soji na Nijar ɗin ya yi ranar Juma’a.
A jawabi da ya yi ta kafar yaɗa labaran ƙasar Kanar Amadou Abdramane ya sanar da hakan da wasu matakan da sojojin suka ɗauka.
“Mun kawo ƙarshen duk wata hulɗar jakadanci da Najeriya da Faransa da Togo da kuma Amurka. Duk wata matsaya da aka cimma a baya ta rushe”.
Tawagar da Ecowas ta tura don tattaunawa da sojojin Nijar ɗin a ƙarƙashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, ta gana da wasu daga cikin sojojin a ranar Alhamis amma ba a cimma wata matsaya ba.
Najeriya da wasu kasashen Afirka dake ƙarƙashin ECOWAS, na tattauna yadda za a iya ɗaukar matakin Soji a ƙasar.
Discussion about this post