Sa’o’i kaɗan bayan Majalisar Ƙolin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ta fitar da sanarwar cewa ba ta goyon bayan a afka wa Nijar da yaƙi, wasu gundun shugabannin ƙungiyoyin addinin Musulunci sun ziyarci Shugaba Bola Tinubu, tare da bada shawarar a yi sulhu da mahukuntan Nijar, ba a fafata yaƙi ba.
Manyan malaman sun kuma nemi iznin Shugaba Tinubu domin su shiga tsakani a sasanta rikicin.
Bayan sun fito daga ganawa da Tinubu, sai Shugaban Ƙungiyar Izala, Sheikh Bala Lau, ya bayyana wa manema labarai cewa ya shawarci Shugaban Ƙasa kada a yi amfani da ƙarfin soja kan Nijar.
“Muna so a bi ta lalama a sulhunta, muna son zaman lafiya da kwanciyar hankali, ba a Najeriya kaɗai ba, har ma a yankin Afrika ta Yamma da duniya baki daya.
“Don haka dukkan malaman nan sun shawarci Shugaban Ƙasa cewa zaman lafiya mu ke so, ba tashin hankali ba.”
Lau ya ce Tinubu ya “yarda” da shawarar su ta su shiga tsakani a matsayin masu yin sulhu a ɓangarorin.
Shi ma Shugaban Ƙungiyar Ansaru, Sheikh Abdurahman Ahmad, ya ce Tinubu ya yi masu alƙawarin cewa, “idan har za mu iya yi wa wancan ɓangaren magana su saurare mu, su yarda da abin da ake so daga ɓangaren su, to shi ma a ɓangaren sa, ECOWAS a shirye ta ke.”
“Idan ba haka kuwa, Tinubu ya ce bai yarda da juyin mulki a yankin Sahel ba, Kuma a matsayin sa na ɗan kishin dimokraɗiyya, zai yi iyakar ƙoƙarin don ya tabbatar da cewa an wanzar da dimokraɗiyya, adalci, ‘yanci da zaman lafiya a ƙasashen ECOWAS.”
Ahmad ya ƙara da cewa Shugaban Najeriya “ya ba mu aikin shiga tsakani mu sasanta, mu tabbatar an cimma daidaito tsakanin ɓangarori biyu na Nijar.”
Bayan fitar su ce kuma Tinubu ya gana da Shugaban Tijjaniya, kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Sanusi Lamiɗo Sanusi.
Kafin nan kuwa, Sanusi, Sarkin Kano na 14, ya je har Yamai ya gana da Shugaban Mulkin Soja, Janar Abdourahmane Tchiani.
“Na zo fadar Shugaban Ƙasa ne domin na sanar da shi abin da na tattauna da shugabannin Nijar.” Haka Sanusi ya shaida wa manema labarai bayan fitowa daga wajen Tinubu.
“Za mu ci gaba da yin bakin ƙoƙarin mu domin mu haɗa ɓangarorin biyu wuri ɗaya su fahimci juna.”
Ya ƙara da cewa batun ƙoƙarin kauce wa yaƙi da Nijar ba abu ba ne da za a bar wa gwamnati ita kaɗai.
Sanusi ya ce duk da dai jami’an gwamnatin Najeriya sun san da tafiyar da Nijar, amma dai ya je ne don kan sa, shi da kan sa ya yi ƙoƙarin ganawa da shugaban na Nijar.
Discussion about this post