Shugaban Juyin Mulkin Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani, ya yi wa tawagar malaman Najeriya ƙarin haske dangane da dalilin da ya sa bai yarda ya gana da tawagar sulhun da ECOWAS ta tura masa a makon da ya gabata ba.
Cikin wata sanarwa da Sheikh Bala Lau ya sa wa hannu, a Yamai bayan sun gana da Janar Tchiani da sabon Firayi Ministan ƙasar, ya ce sojojin juyin mulkin sun ji haushin yadda ECOWAS ta ƙi sauraren su, kafin ta ba su wa’adi.
Sai dai kuma Lau ya ce Janar Tchiani ya bada haƙuri, tare da cewa ƙofar yin sulhu a buɗe ta ke, domin a sasanta rikicin cikin ruwan sanyi.
Sai dai kuma sanarwar ba ta ce ko Janar Tchiani ya bada haƙurin ƙin ganawa da tawagar AU, UN da kuma US da ya yi ba, ko a’a.
‘Mun Ƙwace Mulki Don Mu Daƙile Barazanar Da Ta Tunkaro Nijar Da Najeriya Ɗungurugum’ – Janar Tchiani
Janar Tchiani ya ce tun farko sun tsara juyin mulkin ne sosai a tsanake, ba don komai ba, sai don su daƙile wata gagarimar barazanar da ta tunkaro Nijar har da Najeriya ita kan ta.
Sai dai kuma ba a bayyana kowace irin barazana ba ce.
Tchiani ya ce Najeriya da Nijar fa ba maƙwauta kaɗai ba ne, ‘yan’uwa ne da za su iya zama su sulhunta saɓanin da ke tsakanin su a cikin lalama.
Bayan taron, jagoran juyin mulkin da malaman sun amince su ƙara faɗaɗa hanyoyin sulhuntawar.
Malaman sun bayyana cewa za su koma gida Najeriya su shaida wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu irin abin da suka tattauna a Nijar.
Tawagar ta ƙunshi Sheikh Ɗahiru Bauchi, wanda ɗan sa Ibrahim Bauchi ya wakilta Kabiru Gombe, Ƙaribu Nasiru Kabara, Yakubu Musa Hassan da wasu malamai da dama.
A wurin taron an kuma nuno wani ɗan Sheikh Ɗahiru Bauchi, mai suna Aminu Ɗahiru Bauchi, ya na yi wa taron jawabi da harshen Faransanci.
‘An Yi Gaggawar Ƙaƙaba Wa Nijar Takunkumi, Shi Ya Sa Ta Yi Biris Da ECOWAS’ – Firayi Ministan Nijar
Sabon Firayi Ministan Nijar da Sojojin Mulki su ka naɗa farkon makon da ya gabata, ya bayyana cewa Nijar ta fusata ne da tawagar da ECOWAS ta aika, saboda an yi gaggawar ƙaƙaba mata takunkumi.
Ya ce kamata ya yi a bada ƙofar zaman sulhu da fahimtar juna tukunna, amma sai aka yi gaggawar yanke masu wuta da kuma sauran matakan ƙuntata wa ƙasar, ciki har da bayar da wa’adin mako ɗaya su sauka daga kan mulki.
Discussion about this post