Tsohon gwamnan Kano, shugaban APC na rikon kwarya, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa ba shi da masaniya game da yadda shugaban Kasa Bola Tinubu ya saka sunan Maryam Shetty cikin sunayen ministocin sa ba.
Ganduje ya ce kama yadda kowa ya ga sunanta a jarida haka shima ya gani.
” Ni ko saninta cancan ban yi ba, kawai na ga sunan ta ne. Jim kadan bayan haka sai shugaba Tinubu ya kira ni ya ce wa ya saka sunanta ta cikin sunayen ministoci?
” Na ce masa ban sani ba ni ma. Daga nan ne ya ce lallai a canja ta domin irin abinda ya ji ana faɗi game da ita a shafukan sada zumunta.
Ganduje ya ce ” Da ya ke muna da mata hazikai wanda suka yi aiki da mu a jihar Kano, sai muka mika sunan Mairiga Mahmud.kuma tuni har an tantance ta a majalisar.
Sai dai daga baya shugaba Tinubu ya nada ta mai bashi shawara kan harkokin al’adu da nishaɗi.
Da yawa mutane musamman Kanawa na cewa ba ta cancanta a yi mata misista ba daga Kano ganin irin hazika da ake da su ƴan asalin jihar Kano.
Discussion about this post