Za iya cewa zaman Kwamitin Majalisar Tarayya mai binciken harƙallar ɗaukar ma’aikata a Hukumar Daidaiton Ɗaukar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, ya zama zaman tonon silili.
A zaman da kwamitin ya yi a ranar Talata, tsohon Hadimin Shugabar Hukumar Daidaiton Ɗaukar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, mai suna Haruna Kolo, ya fallasa yadda Shugabar Hukumar, Muheeba Ɗankaka, cewa ita ce ta riƙa ba shi takardun shaidar ɗaukar aikin Gwamnatin Tarayya, ya na sayarwa, kuma ya na kai mata kuɗin har gida.
A ranar Litinin Kolo ya yi wannan bayani a gaban kwamitin majalisar tarayya, mai binciken harƙallar ɗauka aiki a hukumomin gwamnatin tarayya.
A shaidar da Kolo ya bayar, ya ce Muheeba Ɗankaka ce ta naɗa shi gogarman masu yi mata dillancin sayar da takardun ɗauka masu neman aiki, su na karɓar maƙudan kuɗaɗe daga hannun su.
Ya ce ana tura kuɗaɗen ta cikin asusun ajiyar sa na banki, amma ita sai dai ya je POS ya cira ya kai mata har gida.
“Ita Shugabar Hukumar ce da kan ta, ta wakilta ni da haɗa kai da wani Shehu, wanda direba ne kuma PA na wani kwamishinan jihar Taraba.
“Aiki na shi ne ina duk wanda za a ɗauka aiki, Ni ke kai wanda aka ɗauka IPPIS domin a yi masa rajista a manhajar sunayen masu karɓar albashi. Kuma dama ita ce kaɗai ke sa hannu a takardar shaidar ɗaukar ma’aikaci. Idan ta sa hannu, ni ke kaiwa Ofishin Akanta Janar, domin a shigar da shi jerin masu karɓar albashi (IPPS).
“Duk wanda za a ɗauka aiki, sai ya biya kuɗi ta asusun ajiyar banki na tukunna. Ba sanin daga inda su ke na ke yi ba, amma Shehu ne ke kawo su a wuri na. Wasu su kan biya Naira miliyan 1, wasu har Naira miliyan 1 da 500,000, a asusun ajiya ta da ke Eco Bank.
“To amma ita idan ta tashi karɓar kuɗaɗen, sai na je POS na ciro ruwan kuɗi na kai mata har gida.” Inji Kolo.
Ya ce Muheeba Ɗankaka ta yi masa sakayya da samar masa aiki a Hukumar Kula da Kamfanonin Gwamnatin Tarayya (AMCON), shi da wasu mutum uku.
Ya ce a cikin waɗanda aka ɗauka aikin har da wani ƙarin ita shugabar hukumar.
“Cikin waɗanda ta samar wa aiki a AMCON ɗin kuwa, a cikin mu akwai wata mai suna Khadijah Olushola. Amma ita Khadijah ba a ɗauke ta ba. Sai Shugabar Hukuma ta zarge ni wai ni ne na shirya makircin da ya yi sanadiyyar ƙin ɗaukar ƙanwar ta aikin.”
‘Rayuwa Ta Na Cikin Hatsari’ – Kolo Bayan Ya Fallasa Ogar Sa:
Kolo ya shaida wa kamfanin bincike cewa rayuwar sa na cikin hatsari, don haka duk abin da ya same shi a tuhumi Muheeba, Shugabar FCC.
Muheeba na fuskantar zargin cuwa-cuwa, harƙallar kuɗaɗe, ƙabilanci da yin gaban-gabarar handame komai ta hanyar yin yadda ta ga dama a FCC.
Yawancin masu zargin na ta kuwa duk kwamishinonin hukumar ne da ke ƙarƙashin ta.
Rantsuwar Kaffarar Shugabar FCC A Gaban Kwamitin Bincike:
Sai dai kuma Muheeba Ɗankaka ta ƙaryata zarge-zargen da kwamishinonin ya ke mata, tare da cewa su ne masu karɓar rashawa, don ta na yaƙi da su ne, shi ya sa suke mata sharri.
Dangane da Kolo kuwa, yayin da ya ke jawabi har ya kai daidai inda ya ce ya na ɗaukar kuɗi ya na kai mata har gida, sai Muheeba ta yi sararaf ta ɗauki wani Alƙur’ani da ke gefen ta, ta riƙa kwarara rantsuwa cewa ƙarya ya ke mata.
“Na rantse da Allah ban taɓa karɓar ko naira ɗaya daga hannun Kolo ba. Kuma ba ya zuwa gida na.” Inji ta.
‘Kai Kolo Kamata Ya Yi A Ce An Damƙe Ka, Ka Na Kulle’ – Yusuf Gagdi, Shugaban Kwamiti:
Bayan Haruna Kolo ya kammala jawabin sa, sai Shugaban Kwamitin Bincike, Honorabul Yusuf Gagdi, ya dube shi ya ce, “irin wannan harƙalla ka yi har kai da kan ka ka bayyana mana kuɗaɗen da ka ajiye na harƙalla a asusun ka, to kamata ya yi a ce an kama ka, an tsare.
“Amma dai yanzu ina tabbatar maka, ba wanda zai kama ka. Ku dawo gobe Laraba a ci gaba da bayani. Aikin mu shi ne a gano mai laifi kowane, don a hukunta shi. Idan har kai Haruna Kolo ka na da laifi, to ba za ka tsira ba.”
Discussion about this post