An bayyana cewa a duniya kakaf, Najeriya ce ƙasa ta bakwai wajen yawan masu amfani da wayar hannu, wato wayar selula. Haka kuma ita ce ƙasa ta 11 a jerin masu yawan amfani da intanet a duniya.
Mataimakin Shugaban Hukumar Sadarwa ta Ƙasa, Umar Ɗambatta ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke magana wurin buɗe taron kwanaki biyu a kan bunƙasar kayan fasaha a hanyoyin sadarwa na tarho, ranar Alhamis, a Abuja.
Ya ce Najeriya uwa ce sosai a harkokin sadarwar wayoyin tarho a Afirka.
“Kashi 82 na masu amfani da harkokin sadarwar tarho na Afrika a Najeriya su ke. Kuma kashi 29 bisa 100 na masu amfani da intanet a Afirka, duk a Najeriya su ke.
“Ƙasar mu ta 11 a jerin ƙasashen da ke amfani da intanet a duniya. Kuma Najeriya dai ce ta 7 a yawan mutanen da ke amfani da wayar hannu a duniya.”
Sai dai kuma ya ce a ɓangaren ƙarfin intanet kuwa, Najeriya ta zo ta 109 a cikin ƙasashe 131, lamarin da ya ce babban ƙalubale ne matuƙa.
A wurin taron, Ɗambatta ya samu wakilci ne daga Abraham Osahadami, Shugaban Kula da Data Sashen Data, ta Spectrum.
Ya ce cikin shekaru kaɗan da su ka gabata zuwa yau, an samu gagarimin ci gaba a ƙasar nan ta fannin sadarwar zamani.
Don haka ya ke kira da ci gaba da tashi haiƙan a tsaye ana cin moriya da yin amfani da damammakin da ake samu a fannonin sadarwa.
Discussion about this post