Daya daga cikin wadanda suka bayyana gaban sanatocin Najeriya domin a tantancesu, ta barke da kuka tun kafin a yi mata tambaya ko da guda daya ne.
Hannatu Musawa wacce yar asalin jihar Katsina ce ta barke da kuka ne a lokacin da aka ce ta ba da takaitaccen tarihin ta a zauren majalisar.
Sai dai farawar ta ke da wuya sai ta fara zubda hawaye.
Hannatu ta ce ” Iyaye na matalautane fitik, na taso cikin talauci ne. Mahaifina sana’ar saida goro ya ke yi, da da wannan sana’a ce ya tura mu makaranta har nazama abinda nakai a yanzu.
” Na so a ce yana da rai yau yaga wai ni Hannatu ana tantance ni za a yi min minista a Najeriya. Wannan Abu da yayi min dadi.
Sai dai kuma tun kafin a fara mata tambayoyi, sai sanatocin suka bukaci a yi mata sassauci a kyale ta ta tafi abinta.
Daga nan sai aka umarce ta ta tafi abinta ba tare da an yi mata koda tambaya guda daya bane.
Kafin Shugaban Kasa Bola Tinubu ya aika da sunanta domin zama minista, ya nada ta mai ba shi shawara kan harkokin al’adu ada shakatawa.
Discussion about this post