Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce tabbas ECOWAS na nan kan bakan ta na yi wa sojojin juyin mulki a Nijar diran mikiya, ba a janye yiwuwar haka ba tukunna.
Kakakin fadar shugaban kasa Ajuri Ngelale, ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata daga fadar shugaban kasa.
Sanarwar ta ce ECOWAS ta saka talala da dakatar da duk wata musayar kuɗi daga babban bankin Najeriya CBN a kan duk wani da ke da hannu a wannan juyin mulki da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar.
ECOWAS za ta gana ranar Alhamis a Abuja.
Discussion about this post