Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Olusesan Adebiyi matsayin Babban Sakataren Fadar Shugaban Ƙasa, domin ya maye gurbin Tijjani Umar.
Naɗin da Tinubu ya yi wa Adebiyi ya zo ne daidai lokacin ritayar Umar.
Tuni dai Adebiyi dai ya fara aiki a ranar Litinin, tare da jaddada cewa zai yi aiki tuƙuru wajen ganin samun nasarar Shugaba Bola Tinubu.
A lokacin bukin miƙa aiki ga Adebiyi a Fadar Shugaban Ƙasa, Adebiyi ya gode wa Tijjani Umar, wanda ya riƙe muƙamin ya amsa a hannun sa.
Ya jinjina wa irin aiki tuƙurun da Umar ya yi a fadar shugaban ƙasa da kuma ƙasa baki ɗaya, kafin ritayar sa a ranar 10 Ga Agusta.
Shi dai Adebiyi, kafin a maida shi Fadar Shugaban Ƙasa, shi ne Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Lafiya ta Ƙasa.
Ya yi kira ga ɗaukacin ma’aikatan fadar shugaban ƙasa su yi aiki tare a matsayin wani gungun ƙwararrun ma’aikata masu kishin ƙasa.
Shi kuma Umar ya nuna farin cikin sa ganin yadda a cikin shekaru uku ya yi aiki da Shugabannin ƙasa biyu, wato Muhammadu Buhari da kuma Bola Tinubu.
Ya zama Babban Sakataren Fadar Shugaban Ƙasa a ranar 5 Ga Afrilu, 2020 zuwa 10 Ga Agusta, 2023.
Discussion about this post