Shugaban kasa Bola Tinubu, ya cire sunan maryam Shetty, daga jihar Kano daga cikin jerin sunayen waɗanda zai naɗa ministoci.
Shugaban majalisar dattawa, Godwill Akpabio ne ya sanar da haka a lokacin da ya ke karanta wasikar haka a zauren majalisa.
Tinubu ya musanya sunan Maryam Shetty da sunan Mairiga Mahmud, Sannan ya aika da sunan Festus Keyamo shina a tantance shi don zama ministan sa.
Shetty, ta rubuta a shafin ta ta tiwita cewa, da safiyar Juma’a ne aka sanar da ita cire sunanta da Tinubu ya yi.
Ta yi fatan Alkhairi da tabbatar da ci gaba da yin biyayya ga shugaban kasa da kuma duk wata shawara da ya dauka.
“Yanzu aka sanar da ni a zauren majalisar dattawa cewa wai shugaba Tinubu ya cire sunana daga cikin waɗanda za su zamo ministocin sa, an sanar da ni wai ya canja ni da Mariya Mairiga.
“Ina mika godiya ta da fatan alkhairi ga shawara da shugaba na Tinubu ya ɗauka akai na.
A yau Juma’a ana ci gaba da tantance ministocin da shugaba Tinubu ya aika majalisa.
Discussion about this post