Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama Taye Agbaje bisa laifin yi wa ‘ya’yan ɗan uwan sa yankan rago.
Wannan abu ya auku a kauyen Kemta Abata dake Abeokuta jihar Ogun.
PREMIUM TIMES ta samu labarin cewa a ranar 5 ga Agusta Agbaje ya je gidan dan uwan sa
Idowu Agbaje ya tafi da yaran sa ‘yan mata biyu a bisa babur.
Makwabtan da suka ga lokacin da Agbaje ke tafiya da yaran sun ce Agbaje ya tafi da yaran yayin da iyayen basu gida da sunan cewa wai zai Kai su kasuwa.
Da iyayen yaran suka fara neman ‘ya’yan su sai makwabta suka ce sun ga Agbaje da yaran bisa babur.
Da farko Agbaje ya musanta cewa ya san inda yaran suke amma a hannun jami’an tsaro Agbaje ya ce ya yi wa yaran yankan rago kuma ya birne su a wani daji.
Agbaje ya ce ya aikata haka saboda wai ya gano cewa mahaifiyar yaran ta yi masa asiri ta kwashe duk arzikinsa ta ba mijinta.
Kakakin rundunar Omolola Odutola ta tabbatar da haka sannan ta ce Agbaje na tsare a ofishin su.
“Agbaje ya ce ya aikata haka ne saboda ya bi shaidan.
“Tun da ya shiga hannun mu yake ta ihun shaidan.
Odutola ta ce idan sun kammala bincike za su Kai Agbaje kotu domin yanke masa hukunci.
Discussion about this post