Ministan Abuja, Nyesome Wike ya yi zazzafan gargaɗi ga masu harkallar filaye a garin Abuja, cewa karyar su ta kare.
Ministan da ya yi ganawar fara aiki a ofishin sa a yau Litinin ya ce, zai da wao da martabar Abuja kamar yadda aka santa a baya.
” Duk wanda ya san ya mamaye wani wuri na gwamnati da ba a bashi ba ya gina wani abu, ya sani, zan rusa wannan wuri, masu zubar da shara, za su ɗanɗana kuɗar su, waɗanda suke gina dakunan dafa abinci a wuraren shakatawa suma za mu fatattake su
Wike ya ce babu ruwan sa da ko kai wanene ko kuma ka san wani, idan ka yi ba daidai ba ta ka ta kare, zai rugurguza wannan wuri.
”
Discussion about this post