Fitaccen dan wasan kwaikwayo na Hausa Abdullahi Shuaibu, wanda aka fi sani da Karkuzu, ya nemi jama’a su taimaka masa sakamakon lalurar makanta da yake fama da ita.
Karkuzu wanda fitacce ne a shirin wasan Hausa wanda aka riƙa haskawa a shekarun baya da ake kira Karkuzu na Bodara Ikon Allah yana cikin mawuyacin hali yanzu haka.
Shafin Zinariya TV ta saka Karkuzu yana rokon al’ummar Annabi su kawo masa ɗauki.
Karkuzu ya ce ” Yanzu haka abinci na neman gagarare ni. Ga rashin gani da fatara da na afka ciki. A taimaka mini jama’an Annabi.”
Wannan ba shine karin farko da wani fitaccen mawaki ko ɗan wasan kwaikwayo zai fito ya nemi taimakon Al’umma ba sabo da halin kuncin rayuwa da ya shiga ba.
Wasu da dama sun rasu wasu kuma na nan cikin raɗaɗin ciwo babu magani, da tsananin yunwa da talauci da suke fama da shi.
Discussion about this post