Yawan hare-hare ta jiragen yaƙin da Sojojin Saman Najeriya su ka juri kai wa sansanonin ‘yan bindiga, hakan ya kai ga manyan shugabannin su a Arewa maso Yamma sun fara roƙo da neman a sasanta, tare da yi masu afuwa daga gwamnatin tarayya.
Majiyar asiri ta sanar da PRNigeria cewa manyan ‘yan bindiga a maɓuyar su daban-daban a dazukan Katsina da Zamfara sun tura tawagar wakilan su a wani taron neman zaman sulhu a ƙauyen Gusami, cikin Ƙaramar Hukumar Birnin Magaji ta Jihar Zamfara.
Daga cikin waɗanda su ka halarci zaman har da wasu gaggan shugabannin ‘yan bindiga da wakilan su, waɗanda su ka haɗa da Usman Ruga Kachallah, Alhaji Shingi da Lauwali Dumɓulu, Shehu Bagiwaye, Shehu Karmuwal da Jarmi Sanda.
Majiyar ta ce, “sun gana ne domin su haɗa ƙarfi wuri ɗaya su nemi a yi sulhu da Gwamnatin Tarayya.
Sun nemi yin hakan ne kuwa ganin yadda Sojojin Saman Najeriya ke ci gaba da ragargazar su a maɓuyar su da sansanonin su.
A zaman da su ka yi dai sun yi alƙawarin ajiye makamai tare da kasa makaman biyu, su bai wa gwamnati rabi, saura rabin kuma su ɓoye don kada wasu da su ka ƙi yin saranda su kai masu hari.
Sun kuma nuna ɓacin rai cewa yayin da su ke ta ƙoƙarin neman yin sulhu da sabbin gwamnatocin su, a gefe ɗaya kuma ana ci gaba da kai masu hare-hare ba ƙaƙƙautawa, lamarin da kashe masu guyawu.
Ya ce hare-haren da sojoji ke kaiwa ana kashe iyalan su, dabbobin su, kuma ana ruguza masu gidajen su da rumbunan ajiyar kayan abincin su.”
A wani taron da su ka yi na baya-bayan nan, shugabannin ‘yan bindigar sun yarda su yi sarandar rabin makaman su.
Sun ce za su turbuɗe sauran rabin makaman a ƙasa, har zuwa lokacin da dukkan sauran ‘yan bindiga su ka yi sarandar na su makaman.
Sun ce za su bayar da rabi su ɓoye rabin ne, saboda su na taron kada wasu ‘yan bindiga a sassan Zamfara da Sokoto masu iyaka da Nijar su juyo su kai masu hari.
Sun kuma nemi a saka ƙungiyoyin Fulani irin su Miyetti Allah MACBAN, a tsarin sulhuntawar da Shirin Afuwar.
Hare-haren Kakkaɓe ‘Yan Bindiga A Sansanin Ado Aliero A Tsaunin Asola, Yankin Tsafe:
An kashe ‘yan bindiga birjik a wasu hare-haren da Sojojin Saman Najeriya su ka kai a sansanin Gogarma Ado Aleru da ke cikin dajin Ƙaramar Hukumar Tsafe, ta Jihar Zamfara.
Dakarun Operation Hadarin Daji ne su ka kai harin, wanda su ke ci gaba da kaiwa babu ƙaƙƙautawa a wasu yankunan Arewa maso Yamma.
Wasu hare-haren baya-bayan nan kuwa an kai su ne a sansanonin ‘yan bindiga a Zurmi, Tsafe, Faskari da kuma Jibiya.
Discussion about this post