Kwamitin Binciken Harƙallar Kuɗaɗen Inshorar Gidaje sun gayyaci kamfanonin inshorar ƙasar nan baki ɗaya, saboda ƙin biyan kuɗaɗen inshorar gidaje daga 2019 har zuwa 2023.
“Cikin 2019, kamfanonin inshora 54 kun ƙi biyan Naira biliyan 267 ga Gwamnatin. Mi na buƙatar su faɗa mana ina kuɗaɗen su ke.
“Sannan kuma waɗannan Naira biliyan 267, kuɗaɗen 2019 ne fa kaɗai, ba a haɗa da kuɗaɗen 2020, 2021, 2023 da 2023 ba.
“A ƙasar nan mu na da dokoki, amma ba mu amfani ko aiki da dokokin, maimakon haka, a kullum sai dai mu riƙa kuka da ƙorafe-ƙorafe.”
Rashin zuba wa Gwamnatin Tarayya waɗannan kuɗaɗen dai karya Dokar Gidaje ta Ƙasa ce (NHF Act), wadda ta ce tilas kamfanonin inshora su riƙa zuba wani kaso na kuɗaɗen su wajen gina gidajen gwamnatin tarayya masu sauƙin kuɗi.
Shugaban Kwamitin Bincike, Dachung Bagos (ɗan PDP daga Jihar Filato), shi ne ya bayyana gayyatar shugabannin kamfanonin inshora ɗin, ranar Talata a Abuja.
Ya ce kamfanonin sun ƙi biyan Naira biliyan 267 a cikin 2019 kaɗai.
Bagos ya ce akasarin kamfanonin inshora na ƙasar nan ba su bin wannan doka sau-da-ƙafa, wadda aka kafa a ƙarƙashin Sashe na 5(2) na Dokar NHF.
Sashe na 5(2) na dokar dai ya tilasta wa kamfanonin inshura cewa za su riƙa zuba kashi 20% cikin 100% a bunƙasa gidaje. Sai kashi 40% na wasu kuɗaɗen duk a ciki.
“Amma kashi 50% na jimillar kuɗaɗen za su tafi ne wajen bunƙasa NHF, ta asusun Bankin Bada Lamuni, wato Federal Mortgage Bank, a kuɗin ruwan da bai wuce kashi 4% bisa 100% ba.
Bagos ya ce ‘yan majalisa na da rekod na dukkan kuɗaɗen da aka biya a ƙarƙashin NHF, sannan ya ce a 2019 kaɗai, sun ƙi zuba har Naira biliyan 267.
Daga nan ya umarci magatakardan kwamiti ya rubuta ya rubuta wasiƙu ga dukkan kamfanonin inshora, ya faɗa masu ranar da kowanen zai bayyana a gaban kwamiti, domin ya yi bayani.
Discussion about this post