Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta jefa Najeriya cikin masifa, don haka wajibin al’ummar jihar Edo ne su tashi tsaye wajen bayar da ta su gudummawar domin ci gaban jihar su.
Yayin da ya ke bayyana cewa gwamnatin tarayya ta jefa Najeriya cikin matsanancin raɗaɗin tsadar rayuwa, Gwamna Obaseki ya ce, “ƙasar nan ta afka cikin gagarimar matsalar tattalin arziki. Ba za mu iya riƙe hannayen mu tsaya jiran taimako daga ƙasar da ba ta iya taimakon mu ba.
“Maimakon haka, za mu yi dukkan abin da za mu iya yi, domin taimaka wa kan mu da kan mu.” Inji Obaseke.
Ya yi wannan kakkausan gargaɗi a ranar Alhamis, yayin da ya ke buɗe wani taron sanin makamar aiki a kan Dokar Mallakar Ƙasa, kamar yadda bayanin ke ƙunshe a cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai, Crusoe Osagie ya aiko wa PREMIUM TIMES.
Shirin Bola Tinubu na bunƙasa tattalin arziki ya jefa miliyoyin ‘yan Najeriya cikin matsanancin halin tsadar rayuwa, musamman tun bayan cire tallafin fetur a ranar 29 Ga Mayu, 2023.
‘Zan Ciyar Da Wanda Ba Ya Iya Ciyar Da Kansa A Edo’ – Obaseki:
Gwamna Obaseki ya ce gwamnatin sa za ta riƙa ciyar da waɗanda ba su da ƙarfin iya ciyar da kan su.
“Za mu riƙa ɗibar kuɗaɗe daga kuɗaɗen shigar da Jihar Edo ke tarawa na harajin cikin gida, mu riƙa kula da waɗanda ba su iya ciyar da kan su. Muna bakin ƙoƙarin mu domin samar wa ‘yan jihar Edo rangwamen rayuwa.
“Idan da gaske muka maida hankali, jihohi za su iya tsayawa da ƙafafuwan su, ba tare da dogara da Abuja ba.
“Ko an ba mu kuɗi daga kason Gwamnatin Tarayya ko ba a ba mu ba, tilas mu rayu a matsayin jiha.”
Discussion about this post