Jihar Kaduna ta rufta cikin tsomomuwar siyasa tun bayan janye wa da tsohon gwamnan jihar ya yi na zama ministan shugaba Bola Tinubu. Ƴan siyasan jihar musamman ƴan APC sun ja da’ga a tsakanin su, musamman waɗanda ke bangaren tsohon gwamna Nasir El-Rufai da kuma na bangaren sabon gwamna Uba Sani.
Mu na kallo kuma mu na bibiyar abubuwan da ke faruwa a jihar da kuma yadda siyasa ke neman raba kawunan gaggan ƴan siyasan jihar musamman ƴaƴan Jam’iyyar APC.
Duk wanda ya ke bibiyar siyasar Kaduna musamman daga lokacin da aka buga gangar siyasa kafin zaɓen 2023 ya san cewa za a tafka dara tsakanin yaran tsohon gwamna El-Rufai da kuma wadanda za su shigo cikin sabuwar gwamnatin Uba Sani idan ya yi nasara. Yanzu da ya yi nasara an fara samun takun saƙa a tsakanin yan siyasan.
Duk inda kaga Uba Sani a lokacin kamfen, za ka ga Yusuf Hamisu, abin kamar Hassan Da Hussaini. Tun a lokacin masu yin nazari suka fara yin fashin baki cewa wannan kusanta ta su, me zai haifar musu, wato da me Uba Sani zai saka wa Hamisu idan ya zama gwamna ganin kamar shima ya wahala a tafiyar. Kwatsam sai ga dama ta samu.
Tabbas, da ace El-Rufai ya amince ya yi minista kamar yadda aka so badun matsalolin da aka samu ba wajen tantance shi, da kila sai dai wani ma’aikatan ko kuma jakada idan ya yi sa’a, ko kuma ya ci gaba da zaman, Hassan da Hussaini da gwamna Uba Sani.
Kamar yadda muka karanta a jaridu, ance El-Rufai ya mika wa Tinubu wanda ya ke so ya maye gurbin sa, wato tsohon kwamishinan sa Jaafaru Sani, amma kuma gwamna Uba ya garzaya ya ce atitur bai yarda da haka ba, Hamisu ya ke so. Duk da cewa gwamnan ya ce ba ayi haka ba, kokari ake a haɗa shi da abokin sa El-Rufai faɗa.
Amma kuma a jihar Kaduna, an raba jiha ne domin wasu dake tare da gwamna sun ci gaba da nuna duk ana tare ko shi Hamisu ko Jaafaru aka ba duk daya ne, ƴan jam’iyya ɗaya ne, abin tambaya anan, me ya kawo hayaƙi babu wuta?
Wannan cakwakiyar duk an saba ji da gani a siyasa a kasar nan, duk karfin ka da isa da kake ji da shi, idan yau aka ce baka kujerar mulki, abinda ya fi dacewa shine ka ja gefe ka kama bakin ka. Domin kida fa ya canja. Tun a karon farko bayan rantsar da gwamna Uba, abu na farko da ya fara yi shine jawo wasu gaggan ƴan adawan El-Rufai ya basu mukamin masu bashi shawara na musamman. Wannan nade nade ya ba mutane da dama mamaki matuka, mutane ba su gane dalilin yin hakan ba daga hawa mulki.
Da yawa-yawan mutane na ganin tunda El-Rufai ba ya son minista, ba shi da ikon cewa lallai ga wanda zai maye gurbin sa, gwamnan jiha shine shugaban jam’iyya kuma shine zai faɗi wanda ya ke so, ya ba shugaban kasa shawara a yi masa kujerar. Tsohon gwamna El-Rufai ya yi zamanin sa ya gama kuma babu wanda ya saka masa baki. Ita haka mulki ya ke. Idan ka yi naka ka gama sai ka karkaɗa ka bar masu zamani su baza shanyar su suma. Duk abinda suka shuka suma abinda za su girbe kenan.
Yanzu dai haƙa ya rage wa mai shiga rijiya. Ga dukkan alamu dai akwai magana babba da har yanzu bai fito ba, amma idan yayi wari duk za mu ji.
Za mu ga shin Jaafaru Sanin za a yi wa minista ko Yusuf Hamisu Mairago.
Discussion about this post