Yayin da ‘yan Najeriya kuka dangane da halin raɗaɗin tsadar rayuwar da ake fama da ita, tun bayan cire tallafin fetur, su kuwa wasu ƙananan hukumomi 23 a jihohin Kebbi, Zamfara da Sokoto, na su raɗaɗin ya zarce na sauran yankunan Arewaci da Kudancin ƙasar nan.
Baya ga tsadar rayuwa da talaucin da ya yi katutu a birane, garuruwa da yankunan karkara, ƙananan hukumomin Isa, Sabon Birni, Gwadabawa, Illela, Tangaza da Goronyo da ke Jihar Sokoto, har sun fara mantawa da abin da ake kira zaman lafiya da kwanciyar hankali. Domin babu ɗayan waɗannan biyun a yankunan su.
A kullum fama su ke yi kan yadda za su tsira, su wayi gari wata safiyar daga hare-haren makasa, mahara, masu garkuwa, satar shanu da samamen da suka jefa rayuwar su cikin masifar tashin hankali.
Bincike ya nuna cewa da yawan mazauna yankunan sun yi gudun hijira, wasu sun bada kai, sun yi saranda su rayu a ƙarƙashin ‘yan bindiga, ta hanyar ƙulla yarjejeniya da ‘yan bindiga, ta hanyar riƙa biyan su harajin tilas.
Masu gudu sun gudu sun gudu sun bar gonakin su. Wasu ƙauyukan sun zama kangaye, ba kowa, saboda kowa ya tsere.
Abubakar Bawa, Kakakin Yaɗa Labaran Gwamnan Sokoto Ahmed Aliyu, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa gwamnati na sane da irin mawuyacin halin da mazauna yankunan ke ciki.
Zamfara, Zangon ‘Yan Bindiga Matsalar Tsaro:
Wani ɗan kishin jama’a a Zamfara mai suna Faruk Shehu, ya ce an tarwatsa ƙauyuka da yawan gaske a cikin ƙananan hukumomi 14 na Jihar Zamfara. “Amma abin ya fi muni yankunan Ƙananan Hukumomin Maru, Anka, Shinkafi, Maradun Zurmi, Gusau da Bunguɗu.”
Ba sai an tsaya dogon bayani a kan Zamfara ba, jihar da kowa ya san can ne ‘yan bindiga su ka fi ƙarfi, yawa, ta’asa da tara muggan makamai.
Rashin Tsaro A Kebbi: Yankin Zuru Ya Yi Asarar Rayuka 2,500 – Bamaiyi An’iko:
A Jihar Kebbi kuwa, Sakataren Ƙungiyar Ci Gaban Zuru, mai suna Bamaiyi An’iko, ya ce aƙalla daga 2019 zuwa 2023, Masautar Zuru ta yi asarar rayuka 2,500 sanadiyyar hare-haren ‘yan ta’adda.
Ya ce an kashe wannan adadin a yankunan Ƙananan Hukumomin Danko, Wasagu, Fakai, Sakaba, da Zuru.
Ya ce wasu ƙauyuka da ke wajen Bena, Danko da Wasagu sun koma a ƙarƙashin ikon ‘yan bindiga. “Wasu a cikin su sun sa hannun yarjejeniya da ‘yan bindiga.”
Wani basaraken gargajiya mai suna Sani Umar-Jaɓɓi, ya ce akwai buƙatar jama’a su ƙara tashi tsaye, sannan kuma ya yi kuka da cewa dalili na yawan jama’a, wadda ita ma ta na haifar da waɗannan matsalolin.
Discussion about this post