Babu shakka Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, bai taɓa karanta labarin kunkuru da wasu gauraka biyu ba, a cikin Magana Jari Ce. Labarin abin da ya faru mai kanu: Fara Koyon Mulki Da Baki, Kafin Ka Fara Koyon Mulki Da Hannu, ya so ya yi kamanceceniya da irin kasassaɓar da Akpabio ke yawan yi, tun daga lokacin da ya ke Gwamnan Jihar Akwa Ibom, har zuwa yanzu da ya zama Shugaban Majalisar Dattawa.
Kalaman na sa kamar gaɓonta, amma kuma ba gaɓo ba ne, ba kuma za a kira shi gaɓotari ba.
Sai dai me, a duk yawancin lokacin da ya kamata ya yi magana mai muhimmanci, babu abin da ke fitowa daga bakin sa sai kasassaɓa, katoɓara ko sakin-baki.
Wani lokaci kuma idan ya kyara wata maganar ba tare da yi mata linzami ba, sai ka rantse da Allah ka ce Akpabio irin gudurmutsun ƙaton ƙauyen nan ne, ko wani zamaturun kartakin ƙauye.
Wani abin ɗaure kai kuma shi ne, Akpabio dai garau ya ke, ballantana a yi tunanin ko wasu albatsutsai, bira’izai ko ƙwanƙwaman cikin kan sa ne ke motsawa, har ya ke irin waɗannan tambotsai a fili.
Ga 6 Daga Kasassaɓar Akpabio:
1. “Ga Naira Miliyan ɗai-ɗai kyauta zan bai wa mayunwatan shugabannin PDP na ƙananan hukumomin Kudu maso Kudu, su je su ci abincin karya-rantsuwa a Mr Biggs.”
CIkin 2013 Akpabio ya yi wannan katoɓara, a gaban talbijin a Fatakwal, lokacin taron PDP na Kudi maso Kudu, a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.
Wannan abin-kunya ta kai ga Gwamnan Ribas na Lokacin, Rotimi Amaechi da Emanuel Uduiaghan na Delta sun fice daga taron saboda kunya, kuma ba su sake komawa ba.
2. Dillancin Maguɗin Zaɓe A 2013: “Ni na sa biro na soke sunan wanda ya yi nasarar zaɓen fidda gwanin takarar sanata, na maye gurbin sa da wanda na ke so, Sanata Aloysius Etok.”
Haka Akpabio ya shaida wa Ministan Yaɗa Labarai na lokacin, Labaran Maku, lokacin da ya kai ziyara Akwa Ibom, sannan Akpabio ya na gwamna.
3. “Yawancin Kwangilolin Ma’aikatar Harkokin Neja Delta duk ‘Yan Majalisa ake ba su na yi.”
Haka ya furta cikin 2020, lokacin ya na Ministan Harkokin Neja Delta, a lokacin da Kwamitin Binkice ke binciken sa.
A wurin har aka riƙa ƙwaɓar sa, ana cewa, “Minista ya isa haka, kashe makirfo ɗin ka.”
4. “Ka ji tsoron Allah, ka ji tsoron bindiga, ka ji tsoron gwamnati.”
Cikin Mayu ne Akpabio ya yi wannan kasassaɓa a otal ɗin Hilton, Abuja, lokacin da ya ke ta ƙoƙarin neman zama Shugaban Majalisar Dattawa.
A wurin, Kakakin Majalisar Tarayya na lokacin, Femi Gbajabiamila ne ya ke ganawa da zaɓaɓɓun ‘yan majalisa, domin ya ja hankalin su da su goyi bayan wanda Tinubu ke so ya zama Kakakin Majalisar Tarayya.
Akpabio: “Mahaifiya ta ta taɓa ce min, a rayuwa ta ta yau da kullum, na ji tsoron Ubangiji, na biyu na ji tsoron Bindiga, na uku, na ji tsoron Gwamnati. To ku ma Allah ya sa ku ji wannan nasiha da gargaɗin da mahaifiyar tawa ta taɓa yi min.”
5. “Duk abin da kuɗi ya kasa magancewa, idan ana ƙara danƙara kuɗin, za su magance.”
Haka ya taɓa furtawa lokacin ya na Gwamnan Akwa Ibom.
6. “Kowane Sanata ya duba asusun sa, an tura masa kuɗin shan shan shagali a lokacin hutu.”
Wannan shi ne kalamin sa na baya-bayan nan, makonni biyu da suka wuce a majalisa. Bayan an nusar da shi irin kasassaɓar da ya yi, sai ya waske ya ce: “kowane Sanata ya duba i-mel, an turo masa addu’o’i.”
Discussion about this post