Shugaban Riƙon Hukumar Kwastan ta Ƙasa, Bashir Adeniyi, ya yi wa Jami’an Hana Fasa-ƙwauri gargaɗin cewa a sa ido kan iyakokin Najeriya da Jamhuriyar, yayin da Najeriya ke ci gaba da nazarin yadda ake ciki a Jamhuriyar Nijar.
Adeniyi ya yi wannan kiran ne, a lokacin da ya kai ziyara ofishin Kwastan na Jihar Ogun.
Tun bayan juyin mulkin da aka yi a Nijar, inda sojoji suka hamɓaras da Bazoum, sai Najeriya ta kulle kan iyakokin ta da Nijar.
Hakan ɗaya ne daga cikin matakan ƙaƙaba Nijar takunkumin tilasta komawa kan turbar dimokraɗiyya, ta maida Bazoum bisa matsayin shugaban mulkin farar hula.
Haka nan kuma shugaban na Kwastan ya ce a dakatar da kowace motar da ta ɗauki kaya za ta shiga Nijar.
Haka dai ya furta a ziyarar sa hedikwatar Kwastan ta Jihar Ogun da ke Idiroko.
Ya ce akwai yiwuwar masu laifin da ke shiga da makamai cikin Nijar, za su iya yin amfani da wannan hanya ta cikin Jamhuriyar Benin da Kamaru.
Ya gargaɗi Kwastan su sa ido, kada su yi sakacin da za su bari Najeriya ta fuskanci wata sabuwar barazanar tsaro.
“Ya zama tilas a ƙara tashi tsaye a sa-ido. Duk da dai kwanan nan na kai ziyara wasu kan iyakokin, kuma na gamsu 100 bisa 100 dangane da yadda ake aiki.”
Discussion about this post