Jakadan Rasha a Najeriya, Alexei Shebarshin, ya jaddada cewa ƙasar Rasha ba ta goyon bayan duk wani mataki da wata ƙasa ko gungun ƙasashe za su ɗauka domin afka wa Jamhuriyar Nijar da yaƙi.
Shebarshin ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a Abuja, yayin da kuma ya ce amma ƙasar ba za ta tura dakarun ta zuwa Nijar domin goyon bayan gwamnatin mulkin sojan ƙasar ba.
“Rasha ba ta goyon bayan yin amfani da ƙarfin soja kan sabuwar gwamnatin soja ta Nijar. Kuma ba za ta nuna goyon baya ga gwamnatin ta yadda za ta kai sojojin ƙasar ta a ƙasar ba.”
Haka ya bayyana a shafin ofishin, wanda aka tura bayanan har a ofishin PREMIUM TIMES.
An dai riƙa yayata cewa Rasha za ta goyi bayan Nijar idan Sojojin ECOWAS suka kai wa ƙasar farmaki, domin su kawar da sabuwar gwamnatin soja, su maida hamɓararren shugaban ƙasa, Mohammed Bazoum.
An kuma ga yadda masu zanga-zanga a Nijar ke filfila tutar Rasha, lokacin da suka kai wa ofishin Jakadancin Faransa da ke birnin Yamai hari.
Ya shawarci Nijar ta magance matsalolin da ke dabaibaye da su, ba tare da yin amfani da ƙarfin soja ba.
PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Burkina Faso, Mali da Gini za su za su taya Nijar ragargazar kasashen da za su kai wa Nijar hari.
A wani sabon rudani dangane da rikicin da ya biyo bayan juyin mulkin sojoji a Nijar, kasashen Burkina Faso, Mali da Gini sun nuna goyon bayan su ga Nijar, tare da alkawarin za su taya Nijar ragargazar kasashen da za su kai wa Nijar hari
Burkina Faso da Mali sun fitar da sanarwar hadin guiwa a tsakanin su, cewa su na gargadin kada a kuskura a kai wa Nijar farmakin soja, domin duk wanda ya yi amfani da karfin sojoji a Nijar, to tamkar ya kai wa kasashen biyu ne hari.
Sun ce amfani da karfin soja a Nijar zai iya ragargaza yankin Afrika ta Yamma baki dayan sa.
Kasashen biyu sun karanta wannan gargadin a gidajen radiyo da talbijin na kasashen biyu, kwana daya bayan Kungiyar ECOWAS ta yi gargadin yin amfani da karfin soja kan gwamnatin mulkin soja ta Nijar, wadda ta kwace mulki a hannun gwamnatin Mohammed Bazoum.
Sannan kuma sun bayyana cewa duk wani takunkumi da za a kakaba wa Nijar, to rashin adalci ce, rashin tausayin al’umma ne, kuma rashin kunya ce.
Ita ma kasar Gini ta yi sanarwar nuna goyon baya ga gwamnatin mulkin soja ta Nijar. Sanarwar ta ja hankalin kasashen Afrika ta Yamma da su karfafa dankon dangantakar ‘yan’uwantakar da ke a tsakanin su.
Haka dai Shugaban Mulkin Sojan Gini, Kanar Mamadi Doumbouya ya bayyana a cikin sanarwar.
Haka kuma Gini ta ce za ta taimaka wa Nijar ta kowace hanyar da ta dace, tare da tsame kan ta daga kokarin kakaba wa Nijar takunkumi da ECOWAS ke shirin yi.
Yanzu dai Nijar na karkashin Janar Abdourahamane Tchiani, tsohon Shugaban Dakarun Tsaron Fadar Shugaban Kasa.
Ya ce sun hambarar da Bazoum ne saboda rashin iya yin wani katabus a fannin matsalar tsaro da barazanar ‘yan Boko Haram bangaren Al-kaida da ISIS a Nijar.
A wata sabuwa kuma, tuni sojojin Nijar masu rike da gwwamnati sun fara damke hambararrun masu rike da gwamnatin da suka hambaras.
Sun kama Ministan Ma’adinai, Ministan Harkokin Man Fetur, Ministan Harkokin Cikin Gida, Ministan Sufuri da Ministan Tsaro.
Haka kuma sun damke tsohon shuggaban jam’iyya mai mulki wadda suka hambaras, wato PNDS.
Discussion about this post