A yau ne Manyan Hafsoshin Tsaron Ƙasashen ECOWAS za su fara taro a Ghana, domin tattauna batun tura sojojin yankin su afka wa Nijar, domin dawo da mulkin dimokraɗiyya a ƙasar.
A ranar Alhamis ɗin makon jiya ce suka bayyana fara shirin shirya rundunonin afka wa Nijar da yaƙi, idan tattaunawa cikin ruwan sanyi ta faskara.
Za su shafe kwanaki biyu su na taro a Accra, babban birnin ƙasar Ghana, daga Alhamis zuwa Juma’a, domin tattaunawar shirye-shiryen ƙarshe na tada Rundunar Ko-ta-kwana.
Sai dai kuma abin mamakin shi ne yadda Manyan Hafsoshin Tsaron ECOWAS ɗin ke taro a Ghana, kwanaki kaɗan bayan tawagar malaman Musulunci daga Najeriya sun je Yamai, inda su ka tattauna da shugaban mulkin soja, Janar Abdourahmane Tciani da sabon Firayi Ministan ƙasar.
A taron dai sojojin juyin mulkin Nijar sun ce a shirye su ke a sasanta.
Discussion about this post