Ƙungiyar Ƙasashen Afrika, AU ta bayyana cewa ta na goyon bayan dukkan matakan da ECOWAS ta ɗauka domin dawo da dimokraɗiyya a Jamhuriyar Nijar.
Shugaban AU Moussa Mahamat, ya nuna goyon bayan sa kan matakan da ECOWAS ta ɗauka, domin maida Nijar bisa turbar dimokraɗiyya.
Moussa Faki Mahamat ya nuna wannan goyon baya a cikin wata sanarwar da ya fitar.
A ranar Alhamis ce dai ECOWAS ya gudanar da taron gaggawa kan matsalar Nijar, tare da yin kira ga AU ta goyi bayan dukkan tsauraran matakan da ECOWAS ɗin ta ɗauka a kan sojojin juyin mulkin Nijar.
Haka kuma AU ta bayyana cewa tsare Shugaban Ƙasa Mohammed Bazoum ta’addanci ne, kuma tamkar yin garkuwa da shi ne. “Don haka, ba za mu yarda da ci gaba da tsare shi da iyalin sa da ake yi ba.”
“Ci gaba da tsare Bazoum da kunnen-uwar-shegu da mahukuntan sojojin Nijar ke ci gaba da yi, abu ne mai ƙara rura wutar rikicin.” Cewar sanarwar.
Daga nan sai AU ta nemi a gaggauta sakin Bazoum da iyala sa da kuma jami’an gwamnatin sa da su ma ke tsare.
Ita ma Amurka ta goyi bayan ECOWAS, ta ce kada sojojin Nijar su kuskura su taɓa lafiyar Bazoum.
Amurka ta bayyana cewa ta na goyon bayan dukkan matakan da ECOWAS ta ɗauka da wanda za ta ɗauka nan gaba kan mahukuntan sojojin juyin mulkin Nijar.
Ta ƙara da cewa kada mahukuntan sojoji su kuskura su bari wani abu ya taɓa rayuka da lafiyar Shugaban Ƙasar Nijar na dimokraɗiyya, Mohammed Bazoum da iyalin sa da sauran jiga-jigan gwamnatin sa waɗanda ke tsare.
“Amurka ta bi sahun ECOWAS wajen kira da a gaggauta komawa kan turbar dimokraɗiyya a Nijar”, haka Sakataren Harkokin Waje na Amurka, Antony Blinken ya bayyana.
Kwanan nan Amirka ta dakatar da wani tallafin da ta ke bai wa Nijar, bayan sojoji sun ƙwace mulki a ƙasar.
A ranar Alhamis ce kuma ECOWAS ta ce dakarun ta su fara shirye-shiryen ko-ta-kwanan yaƙi da Nijar.
Ta ce ta na so a sulhunta da lalama, amma kuma ba ta fidda ran za a gwabza yaƙi ba.
Blinken ya ce Amurka na so a sulhunta cikin ruwan-sanyi.
Ana zaman ɗarɗar a Nijar, ƙasa mai arzikin sinadaran yuraniyan. Kafin juyin mulki dai Nijar na da kyakkyawar alaƙa da Turawan Yamma, a yaƙi da ta’addanci a yankin Sahel.
Discussion about this post