Shugaba Bola Tinubu ya bayyana juyin mulkin da ya faru yau Lahadi a Gabon da cewa wata ‘annobar ƙarfa-ƙarfa ce wadda ke bazuwa a cikin Afrika.
Tinubu wanda shi ne Shugaban ECOWAS, ya ce ya na kallon dukkan abin da ke faruwa a Gabon, kuma shi da sauran shugabannin Afrika za su yi tsayuwar daka wajen kare dimokraɗiyya a Afirka.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran Tinubu, Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Laraba, a Abuja, ya ce Tinubu wanda ya taɓa sadaukar da rayuwar sa wajen kare dimokraɗiyya, ya yi amanna mulki a hannun jama’a ya ke, kuma su ne ke da haƙƙin zaɓen shugaban su, ba a yi masu ƙarfa-ƙarfa da bakin bindiga ba.
PREMIUM TIMES Hausa ta bada labarin an kifar da gwamnatin Ali Bango a Gabon, bayan sojoji sun yi zargin yin maguɗi a zaɓen shugaban ƙasa.
Sojojin dai sun kifar da gwamnatin Gabon, sun ce an tafka maguɗi a zaɓen shugaban ƙasa.
Manyan Hafsoshin Sojojin Gabon sun kifar da Gwamnatin dimokraɗiyya a ƙasar, bisa dalilin su na cewa an tafka maguɗi a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ƙasar.
Juyin mulkin Gabon shi ne juyin mulki na bakwai a ƙasashen Afrika tun daga 2019.
Rahotanni sun tabbatar da cewa sojojin Gabon sun yi wannan sanarwa da jijjifin safiyar yau Laraba, a gidan talabijin na ƙasar.
“Mun yi wannan juyin mulki domin cewa al’ummar ƙasar Gabon. Mun yanke shawarar karɓar mulki domin mu kare zaman lafiya da kauce wa tashin hankali a ƙasar nan.” Haka Aljazeera ta ruwaito sojojin sun bayyana.
Sun kuma ce sun ƙwace mulkin ne daga hannun farar hula, saboda an tafka gagarimin maguɗi a zaɓen shugaban ƙasa da aka yi a ranar Asabar da ta gabata a ƙasar.
Cikin sanarwar da su ka bayar, Sojojin Mulkin Gabon sun rushe zaɓen da aka gudanar, sun kori dukkan shugabannin mulkin siyasa kuma sun rufe dukkan kan iyakokin ƙasar.
A ranar Asabar ce aka yi zaɓen shugaban ƙasa a gaban, wanda ya haifar da ruɗani, bayan an bayyana cewa Shugaba Ali Bongo ne ya yi nasara a zangon mulkin sa na uku a jere.
Ali Bongo ya zama tun cikin 2009, bayan mutuwar mahaifin sa, Omar Bango.
A zaɓen ranar Asabar, Hukumar Zaɓen Gabon ta ce Ali Bango ya samu kashi 64.27 na yawan ƙuri’un da aka kaɗa. Amma ɗan adawar sa Albert Ondo Ossa ya samu kashi 30.77.” An dai ɗauki tsawon lokaci ana kunge-kunge kafin a bayyana sakamakon zaɓen.
Rahotanni sun ce an ji ƙararrakin harbin bindiga a babban birnin Gabon, Libreville. Kuma ba a san inda shugaban ƙasar ya ke ko halin da ya ke ciki ba.
Juyin mulkin ya zo wata ɗaya daidai bayan juyin mulkin Nijar. Kuma mako ɗaya bayan AU ta kafa wa Sojojin Mulkin Nijar takunkumi, tare da dakatar da ƙasar daga kasancewar ta mamba a AU.
Discussion about this post