Sojojin Mulkin Gabon, sun bayyana cewa su na tsare da Nourriden Bongo Valentin, ɗan hamɓararren Shugaban Ƙasa Ali Bongo.
Sun ce su na tsare da shi ne da wasu mutane shida, bisa zargin su da cin amanar ƙasa.
Yayin da mahukunta a ƙasar ba su bayyana irin cin amanar ƙasar da su ka yi ba.
Amma kuma Aljazeera ta ruwaito cewa ana zargin su Nouriden ne da laifin baddala sakamakon zaɓe, inda su ka kayar da jam’iyyar adawa.
Yayin da su kuma Sojojin Mulki, sun ce hamɓararren shugaban ƙasa ɗin ya na tsare a cikin gidan sa, tare da iyalan sa da kuma likotocin sa.
Sun ce waɗanda za a tuhuma ɗin sun ci amanar ƙasa, lamarin da ake ganin cewa zargin su ake yi da baddala sakamakon zaɓe, murɗiya da kuma maguɗin zaɓe.
Ali Bongo, hamɓararren Shugaban Ƙasa, ya yi takara da ‘yan hamayya 18, amma kafin zaɓe sai su ka ragu, su ka mara wa sauran ‘yan adawa shida baya domin a kayar da Bango.
Hukumar Zaɓen Gabon ta sanar da nasarar Ali Bongo da kashi sama da 64, na biyu kuma da kashi sama da 33. Lamarin da aka ce an yi gagarimin maguɗi.
Ali Bango ya hau mulki shekaru 14 da su ka gabata, bayan rasuwar mahaifin sa, Omar Bango.
Omar wanda ya hau mulki tun a 1967, ya shafe shekaru 42 ya na mulkin Gabon a cikin tsarin jam’iyya ɗaya tilo. Bai yarda da kafa jam”iyyun adawa a Gabon ba, har sai cikin 1991.
Gabon ƙaramar ƙasa ce mai yawan jama’a miliyan 2.3 kacal. Ta na da arzikin ɗanyen man fetur, domin a kowace rana ana haƙo gangar ɗanyen mai 200,000.
Ita ce ƙasar da ke haƙo ɗanyen mai mafi ƙanƙanta a jerin ƙasashen da ke cikin Ƙungiyar Ƙasashe Masu Arzikin Fetur na Duniya (OPEC).
A cikin shekaru uku kacal, an yi juyin mulki 9 a ƙasashen Afrika Rainon Faransa, waɗanda su ka haɗa da Gini, Mali, Burkina Faso, Chadi, Tunisiya, Nijar da Gabon.
Discussion about this post