Wasu garuruwa a Nijar na fuskantar bakin duhu sakamakon takunkumin da kungiyar ECOWAS ta kakaba mata a ranar Lahadi.
PREMIUM TIMES ta tabbatar da hakan daga wani dan kasuwa da ya ke yin balaguro tsakanin Katsina da Nijar amma nemi a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro cewa matsalar wutar lantarkin da mazauna yankunan kasar Nijar ke fama da shi na da nasaba da takunkumin da aka kakaba wa kasar dalilin juyin mulkin da sojoji suka yi.
BBC ta kuma ruwaito kamfanin samar da wutar lantarki na Niger Nigelec yana cewa Najeriya ta yanke samar da wutar lantarki a kasar. Najeriya dai ita ce ke raba wa kasar wutar lantarki.
Rahotanni sun bayyana cewa, a yau Laraba ne hafsoshin tsaron kasashen ECOWAS na ganawa a Abuja. Sai dai kasashen Mali da Nijar da Guinea Bissau da Burkina Faso da Guinea ba su halarci taron ba.
Bugu da kari, wata tawaga daga kungiyar ECOWAS karkashin jagorancin tsohon shugaban mulkin sojan kasar Abdulsalami Abubakar na yin taro a Nijar a yau Laraba domin ci gaba da shiga tsakani.
A ranar Talata ne Faransa ta fara kwashe ‘yan kasarta da sauran ‘yan kasashen Turai. Ya zuwa lokacin da aka fitar da wannan rahoto, an kwashe akalla Faransawa 350 daga Nijar, in ji ma’aikatar harkokin wajen kasar.
Discussion about this post