Sanatoci sun yi watsi da bukatar da shugaba Bola Tinubu ya yi na neman izinin tura sojojin Najeriya zuwa jamhuriyar Nijar a matsayin wani bangare na rundunar ECOWAS domin maido da zababben shugaban kasar bisa tafarkin dimokuradiyya.
A cewar wani dan majalisar dattawan da ya halarci taron, Sanatocin sun amince da zartas da kudurin yin Allah wadai da juyin mulkin da kuma yabawa shugabannin kungiyar ECOWAS kan kokarin da suke yi na maido da tsarin mulkin Nijar, amma sun yi watsi da zabin a tura sojoji kasar.
Kusan duka Sanatocin sun yi magana kuma sun yi watsi da zabin a tura soja saboda dalilai da yawa da kuma saboda daɗaɗɗiyar dangantakar da ke tsakanin Najeriya da Nijar.
Sanatoci dai sun ce za su zartar da kudiri na yin Allah wadai da juyin mulkin, amma batun tafiya yaki da Nijar ba ma zai taɓa yiwuwa ba.
Discussion about this post